in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kila yawan kallon na'urori masu amfani da lantarki zai kawo illa ga girman kananan yara
2020-07-02 08:21:51 cri

Sakamakon yadda talibijin, kwamfuta ko kuma na'ura mai kwakwalwa, wayar salula da sauran na'urori masu amfani da lantarki suke samun karbuwa a duk fadin duniya, ya sa tsawon lokacin da kananan yara suke dauka wajen yin amfani da wadannan na'urori, ya karu. Wani sabon nazari da aka gudanar a kasar Canada ya nuna cewa, watakila kallon irin wadannan na'urori fiye da kima zai kawo illa ga yadda kananan yara suke girma yadda ya kamata.

Dangane da tsawon lokacin da kananan yara suke dauka wajen kallon wadannan na'urorin a ko wace rana, Madam Zhang Chuji, likita ce da ke aiki a dakin masu bukatar gaggawa a asibitin Tiantan na Beijing ta ba da shawarar cewa, bai kamata ba tsawon lokacin da kananan yara da shekarunsu suka wuce 2 amma ba su kai 6 a duniya ba suke dauka ya wuce awa daya a ko wace rana, ta haka za su iya samun isasshen lokaci na yin harkokin da suka amfani lafiyarsu da yadda suke girma.

Masu nazari daga jami'ar Calgary da jami'ar Waterloo na kasar Canada sun kaddamar da rahoton nazarinsu a kwanan baya cewa, daga watan Oktoban shekarar 2011 zuwa watan Oktoban shekarar 2016, sun tattara bayanai dangane da tsawon lokacin kallon na'urori masu amfani da lantarki da kuma yadda kananan yara suke girma, wadanda suka shafi kananan yara 'yan kasar Canada fiye da dubu 2 da dari 4 da shekarunsu suka wuce 2 amma ba su kai 6 da haihuwa ba, mata da kuma maza.

Masu nazarin sun gano cewa, idan kananan yara da shekarunsu suka kai 2 a duniya sun fiye kallon talibijin da sauran na'urorin lantarki, ba safai suke cin jarrabawa a fannin yadda suke girma ba. Ban da haka kuma, masu nazarin sun kwatanta lokacin da kananan yara da shekarunsu suka kai 3 da haihuwa suka dauka suna kallo da kuma yadda suke girma yayin da shekarunsu suka kai 5 a duniya, sun samu sakamako kusan irin daya.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, nazarinsu ya gano alakar dake tsakanin lokacin kallon irin wadannan na'urori da kuma yadda suke girma, sa'an nan kila kallon na'urorin fiye da kima zai kawo illa ga yadda kananan yara suke girma yadda ya kamata. Sun ba da shawarar cewa, wajibi ne likitoci masu kula da kananan yara da kuma ma'aikatan kiwon lafiya su taimakawa iyaye dangane da yadda 'ya'yansu suke amfani da irin wadannan na'urori masu amfani da lantarki yadda ya kamata, tare da yin tattaunawa da iyayensu game da illolin da 'ya'yansu za su gamu da su sakamakon kallon talibijin da sauran na'urorin lantarki fiye da kima.

Duk da haka masu nazarin sun yi bayani da cewa, ba su yi nazari kan lokacin kallon na'urorin lantarki da kananan yara da shekarunsu ba su kai 2 a duniya ba suka dauka ba, kuma ba su bambance nau'o'in na'urorin lantarki ba. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China