in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Motsa jiki kafin yin karya kumallo yana yin amfani da kitse da yawa
2020-06-07 16:33:49 cri

Wani nazarin da aka gudanar kan wasu mutane a kasar Birtaniya ya yi bayanin cewa, motsa jiki kafin karya kumallo na iya karawa jiki amfani da kitse, kana kuma ya na iya kyautata yadda jikin dan Adam yake samar da sinadarin Insulin, da kuma taimakawa rage barazanar kamuwa da ciwon sukari da ciwon zuciya.

Masu nazari daga Jami'ar Bath ta kasar Birtaniya da jami'ar Birmingham ta kasar sun gudanar da wani nazari cikin makonni 6 cikin hadin gwiwa kan maza 30 masu kiba ko kuma wadanda nauyinsu ya wuce misali. Masu nazarin sun raba wadannan mutane zuwa rukunoni guda 3, inda mutane na rukuni na A suka motsa jiki kafin karya kumallo, mutane na rukuni na B suka motsa jiki bayan da suka karya kumallo, sa'an nan wadanda suke cikin rukuni na C ba su sauya salon zaman rayuwarsu ba. Dukkan wadannan mutane da ke cikin rukunonin 3 sun ci abinci iri daya a matsayin karin kumallo, sun kuma motsa jiki ta hanya iri daya, wato sun dauki awa daya suna hawan kekuna.

Sakamakon nazarin ya nuna mana cewa, in an kwatanta su da wadanda suka motsa jiki bayan da suka karya kumallo, mutanen da suka motsa jiki kafin su yi karin kumallo sun fi amfani da kitsen da ke jikunansu har sau daya. Dalilin da ya sa haka shi ne domin idan an fara motsa jiki da sanyin safiya kafin a karya kumallo, ya zama tilas jikin dan Adam ya fara aikinsa cikin hanzari, ya rubanya kokari, ta yadda zai iya samar da isasshen karfi wajen motsa jiki yadda ya kamata.

Masu nazarin sun yi karin bayani da cewa, ko da yake sauya hanyar motsa jiki cikin makonni 6 ba zai rage nauyin jikin dan Adam da yawa ba, amma zai yi tasiri mai kyau wajen kyautata lafiyar wasu mutane masu ruwa da tsaki, saboda motsa jiki kafin karya kumallo yana iya taimaka wa jikin dan Adam kara samar da sinadarin Insulin yadda ya kamata, ta haka za a iya tabbatar da daidaiton yawan sukarin da ke cikin jinin dan Adam.

Masu nazarin sun ci gaba da cewa, nan gaba za a yi nazari kan tasirin da motsa jiki kafin yin karya kumallo zai yi wa jikin dan Adam cikin dogon lokaci da kuma gano ko zai yi tasiri kan mata kamar yadda ya yi tasiri kan maza. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ga Wasu
v Yin gudu kadan zai taimakawa kiwon lafiya 2020-06-07 16:32:21
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China