Wannan nazari ya hada da kananan nazarce-nazarce guda 14 masu ruwa da tsaki, wadanda suka shafi mutane fiye da dubu 230, kana kuma an dauki shekaru 5 da rabi zuwa shekaru 35 wajen gudanar da wadannan nazarce-nazarce.
Bayan da masu nazari daga jami'ar Victoria ta kasar Australia da dai sauransu suka tantance bayanai masu ruwa da tsaki da aka samu daga wadannan nazarce-nazarce, sun gano cewa, in an kwatanta wadanda ba su yin gudu ko kadan, yawan mutuwar wadanda su kan yi gudu ya yi kasa da kaso 27 cikin dari, sa'an nan kuma, yawan yiwuwar mutuwar wadanda su kan yi gudu sakamakon kamuwa da cututtukan jijjiyoyin zuciya da kwakwalwa ya yi kasa da kashi 30 cikin dari, yawan yiwuwar mutuwarsu sakamakon kamuwa da ciwon sankara ya yi kasa da kaso 23 cikin dari.
Sakamakon nazarin ya yi nuni da cewa, ko da yin gudu sau daya a ko wane mako, kuma tsawon lokacin da aka dauka ana gudu bai kai mintoci 50 a ko wane karo ba, saurin gudu bai kai kilomita 8 a ko wane awa daya ba, dukkansu suna da nasaba da kyautatuwar lafiya da kuma tsawaita rayukan mutane.
Amma duk da haka, yin gudu da yawa ba zai kara amfana wa lafiyar mutane ba. Sakamakon nazarin ya tono cewa, hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa wato WHO ta ba da shawara kan tsawon lokacin motsa jiki a ko wane mako, amma babu wata alaka tsakanin kara yin gudu da kuma kara raguwar mutuwar mutane. Hukumar WHO ta ba da shawara cewa, kamata ya yi baligai su dauki mintoci a kalla 150 suna motsa jiki da matsakaicin karfi a ko wane mako, ko kuma su dauki mintoci a kalla 75 suna motsa jiki da karfi a ko wane mako. (Tasallah Yuan)