A ranar juma'a 26 ga watan February, 2016 ne, na saurari shirin Allah Daya Gari Bambam wanda malamai Mamman Ada da Lubabatu suka gabatar mana inda malaman suka yi tsokaci adangane da wakoki masu dogon tarishi na jama'ar Mangolia ta gida kasar Sin. Babu shakka, wakokin mutanen Mangolia ta gida da masu gabatar da shirin suka kayatar da mu tare da nishadantar da mu da su bisa wakokin jama'ar Mangolia ta gida ta kasar Sin, duk wakokin Mutunen Mangolia ta gida suna da dadi sosai, amma kuma wakar malama Amina wata karamar mawakiya yar kabilar Mangolia, ta fi burgeni sosai kuma na fi jin dadi yadda yakamata. Agaskiya, mun ji dadin yadda malam Mamman Ada da malama Lubabatu suka gabatar da shirin na Allah Daya Gari Bambam.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.