Bayan gaisuwa mai yawa da fatan alheri ga ma'aikatan CRI Hausa baki daya, da fatan an kammala shagulgulan bikin bazara lami lafiya. Hakika, ina mai farin cikin sanar da ku cewa na saurari sabon shirin ku 'Allah daya gari bamban' na yau Jumu'a 19 ga wata, wanda malama Lami ta gabatar dangane da biki na karshe yayin bikin bazara, wato bikin Yuanxiao.
Wannan shiri na yau ya kara min ilimi dangane da bikin bazara yadda ya kamata, domin nayi tsammanin cewa abu mafi muhimmanci yayin bikin bazara shi ne, haduwar iyalai, raba kyaututtuka, da ziyartar muhimman wuraren tarihi da bude idanu. Amma yanzu na fahimci cewa akwai wani wasa na daban mai kyau wanda Sinawa ke gudanarwa a ranar 15 ga watan farko na sabuwar shekara bisa kalandar manoma. Hakika wannan biki na Yuanxiao ya ja hankali na, musamman yadda ake rataye fitilu masu kyan launi a gidaje da koma yadda ake sakar wasu fitilun a cikin iska.
A ra'ayi na, wannan al'ada abin alfahari ce ga Sinawa saboda tana tattare da wasanni masu jan hankali da suka hada da fitilu masu launi iri iri da wasan zaki, da dai sauransu. Ina fatan gwamnatin kasar Sin za ta bayar da kulawa ta musamman ga irin wadannan dadaddun al'adun gargajiya domin ka da guguwar zamani ta yi awon gaba da su.
Mai sauraron ku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners Club
Kanon Dabo, Nigeria