Tare da fatan baki dayan ma'aikatan sashen Hausa suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing kamar yadda na ke lafiya nan birnin Kano.
Bayan haka, na ji dadin sauraron sabon shirin ku na 'Gani Ya Kori Ji' a jiya Laraba 17 ga wata inda malamai Ibrahim Yaya, Maman Ada da Saminu Alhassan suka tattauna muhimmin batu da ya shafi yaduwar makamin nukiliya, wanda aka fi sani da makamin kare dangi.
Kodayake, malamai sun bayyana ra'ayoyin su da suka zo daya wajen jaddada irin hadarin dake tattare da mallakar makamashin nukiliya ko kuma shi kansa uwa - uba makamin na nukiliya. Hakika, a nan, ra'ayi na ya zo daya da na malamai, domin manyan kasashen duniya sun mallaki wannan fusaha ce ta nukiliya domin samar da makamashin wutar lantarki, to amma yin hakan ma yana da hadarin gaske kamar yadda mu ka ga hadarin fashewar tashar makamashin nukiliya da ke wani gari mai suna Chornabyl na kasar Rasha da kuma tashar Fukushima ta kasar Japan bayan da aka samu motsinka kasa yayin ambaliyar ruwa da guguwar iska mai karfi ta Tsunami.
Saboda haka, mallakar wannan fusaha ta nukiliya ko kuma bunkasa ta bisa kowacce manufa babbar barazana ce ga makomar dan Adam. Don haka, ya dace MDD ta bullo da wani sabon kuduri da zai haramtawa kasashen duniya mallaka ko kuma yin amfani da wannan fusaha kwata kwata. Domin idan ba a dakile yaduwa ko bazuwar wannan fusaha ba, to akwai yiwuwar wata rana wannan fusaha za ta iya shiga hannun masu tsatsauran ra'ayi, wato ina nufin 'yan ta'adda. Allah SWT Ya kiyaye, idan wanna fusaha ta shiga hannun su, to kuwa diniya ba za ta gani da kyau ba.
Mai sauraron ku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners Club
Kanon Dabo, Nigeria