Slm.
Ina mai gabatar muku da shawara cewa, yakamata ku kirkiro da wani saban shiri wanda zai maida gurbin tsohon shirinku mai suna Magabatan kasar Sin. Kirkiro da saban shirin zai bada zarafi ga milyoyin masu sauraronku a dukkan nahiyoyi bisa sanin tarishin mashahuran shugabannin kasar Sin wayanda suka nuna kwazo da himma sosai wajen gina sabuwar kasar Sin ta zamani kuma shirin ya kara sanar da masu sauraro hakikanin tarishin kasar Sin da karin bayani adangane da yankuna da tsibiran kasar Sin, kamarsu tsibirin Diaouyu, tsibirin Taiwan na kasar Sin da kuma yankunan Macao da jihar Tibet. Babu shakka, akwai masu saurarenku masu yawa da suke bukatar sanin mashahuran guraren tarishi da kuma guraren yawan shakatawa da bude idanu da sanin yawan kabilun kasar Sin da kuma tarishinsu da dai sauransu. Kana kuma, yana da kyau ku yaye labilen saban shirin da tarishin marigayi madugun gina sabuwar kasar Sin ta zamani wato, Tsohun shagaban jamhuriyar jama'ar Sin ta zamani malam Mao Zadeng.
Wsl.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua, shugaban cri Hausa listener's club na jihar Yobe, Nigeria.