in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cudanyar dake tsakanin Afrika Da Sin
2015-12-04 08:21:31 cri

GABATARWA: Afrika akwai hulda mai kyau tsakanin kasar SIN da Afirka. Kamar huldar auratayya, kasuwanci, zamantakewa da dai sauransu. Huldar auratayya: Tsakanin kasar SIN da Afrika akwai huldar auratayya, inda zaka samu, da dama daga cikin mutanen kasar SIN, na auren mutanen Afrika duk da cewa akwai bambancin al'adu da ke tsakaninsu, amma wannan bai hana 'yan Afrika auren SINAWA ba. Wanda ansha yin wannan aure da dama, sa'annan kuma, sau da dama su ma 'auratan ne musamman mata kan zabi inda zasu zauna, ko a kasar SIN din ko a Afrika, sa'annan yawancin auren ana daurashi ne ko dai a bisa al'adunsu na gargajiya ko kuma a zamanance, kuma galibi ana daura auren ne a gidansu yarinyar. Huldar kasuwanci: Akwai hulda mai kyau ta kasuwanci tsakanin mutanan kasar Sin da Afirka, baya ga tsohuwar alakar cinikayya dake tsakani. A kasar Sin babban birnin kasuwanci kuma cibiyar hada-hada da suke ji da ita wajan saye da sayarwa ita ce Guangzhou, inda acan Birnin Guangzhou, duk abin da ka sani na sana'a ko saidawa a duniya, zaka iya samun sa cikin rahusa. Wannan ta sanya akwai 'yan Afirka da dama acan birnin Guangzhou da suke ta hada-hada ta saye da sayarwa, wannan ta sanya zaka ci karo da dama daga cikin mutanen Afirka sunje kasuwanci, wasu na zaune har da iyalensu suke tare, duk ana kasuwanci, zaka samu 'yan Afirka da dama na sayan kayayyaki, kamarsu kayan abinci, kayan sawa, kayan mata, wayoyi da sauran dangin kayayyakin wutan lantarkironi a farashi mai rahusa, suna turashi Afirka ne domin cin riba mai mai kwawo, haka kuma suma Sinawa din da suke zaune a Afirka zaka samu suna sayan kayayyakin dake can gida Afirka suna turowa don su sana'anta su suma su ci riba.

Huldar Zamantakewa: Akwai huldar zamantakewa mai kyau tsakanin Sinawa da mutanan Afirka, inda zaka samu da dama daga cikin 'yan Afirka suna zaune da iyalensu cikin tsanaki da lumana da kuma amincin amintaka babu tsangwama a zamantakewar al'ummar Afrika da Sinawa, idan har mutum yana da takardu da shaidar zama daga jami'an tsaro ko wanda hukumonin kasar Sin ke bayarwa, to zai yi zamansa lafiya a kasar Sin, har zuwa lokacin da ya keso ko ya debawa kansa, babu tsangwama ba cuta- cutarwa, don haka mutanen kasar Sin, masu kawaici ne da son jama'a, ba ruwansu da nuna bambancin launin fata da wasu al'ummar kasashen keyi ko nuna wariya, don ni tunda na kejin labarin mazauna kasar Sin, kimanin shekara biyar da suka wuce babu wanda ya taba fadamin an nuna masa bambancin cewa shi ba dan kasa bane ko shi daga nahiyar Afirka ne ya fito ko ace bakar fata, sai dai a nuna masa kauna kamar dan kasa. Kuma hakan take a nahiyar Afirka suma Sinawa suna zaune lafiya suna kasuwancinsu babu tsangwama.

Daga karshe ina kira ga 'yan Afirka da in har za suyi kasuwanci to su gaggauta zuwa kasar Sin (Chana) don samun kaya masu kyau, sauki da kuma rahusa kana akwai aminci gwargwadon abin da suke da shi na jari, kaya akwai sauki sosai gashi babu tsangwama. Ya Allah ina rokonka ka bani ikon zuwa kasar SIN domin in gane wa idona labarin da na keji da kuma karanta wa a shafukan sada zumunta Amin.

Daga Adamu Aliyu Ngulde a Jihar Borno ta Nijeriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China