Akwai hulda mai kyau tsakanin kasar SIN da Afirka . Kamar hurdar auratayya, huldar kasuwanci,Da huldar zamantakewa. Huldar auratayya : tsakanin kasar SIN da AFIRKA akwai hurdar auratayya Inda zaka samu da dama daga cikin mutanan birnin SIN na auren mutanen AFIRKA duk da cewa akwai Banbancin al'adu dake tsakani amma wannan baya hana yan AFRIKA auren yan Birnin SIN. Wanda ansha yin wannan aure da dama sannan kuma su ma auratan kan zabi inda zasu zauna ko a cikin birnin SIN din koko a AFIRKA, sannan yawncin auren ana daurashi ne a nan birnin sin a gidansu yarinyar. Huldar kasuwanci: akwai hulda mai kyau na kasuwanci tsakanin birnin Sin da Afirka , a nan Birnin Sin babban jahansu da suke ji da ita wajan kasuwanci shine Guangzhou inda anan Birnin Guangzhou duk abinda kasani a na saidawa a duniya zaka iya samunshi , to yawanci zaka samu akwai yan Afirka da dama anan birnin Guangzhou inda da dama daga cikinsu sunzo kasuwanci ne, zakasamu wasunsu harda iyalensu suke tare duk ana kasuwanci, zaka samu yan Afirka da dama nasayan kayayyaki kamarsu kayan abinci, kayan sawa, kayan mata, wayoyi da dai sauransu a farashi mai rahusa suna turashi kasar Afirka suna cin riba mai yawa, haka kuma suma yan Birnin Sin din dasuke Afirka zaka samu suna sanan kayayyakin dake can gida Afirka suna turowa don suma su ci riba. Huldar Zamantakewa , akwai huldar zamantakewa tsakanin Birnin Sin da Afirka inda zaka samu da dama daga cikin yan Afirka suna zaune da iyalensu lami lafia babu tsangwama a cikin birnin Sin, mutum in har yana da shaidan zama da jamian tsaron birnin sin ke bayarwa to zai iya zama a birnin Sin har iya lokacin da yakeso babu tsangwama, don mutanen birnin Sin masu kawaicine ga son jamaa ba ruwansu da nuna banbanci, don ni tunda nake zaune a nan birnin Sin yau kusan shekara uku bawanda ya taba nunamin babancin cewa ni ba dan kasa bane, aa saidai a jawoni a jiki kamar dan kasa. To hakanan a Afirka suma yan birnin Sin suna zaune lami lafiya suna aikinsu babu tsangwama. Daga karshe ina mai kira ga yan Afirka da in har zasuyi kasuwanci to suzo birnin Sin don a birnin sin akwai rahusa sosai gashi babu tsangwama. Allah yamana jagora Amin.
Hussaini Ibrahim Gebi