Kuma abun sha'awar sai ga wata kasa da ake ganin duk duniya babu inda ya kaita nisa musamman daga nahiyar Afurika, wato kasar sin suka zabo harshen hausa domin su nunawa duniya suna son harshen. Kuma ba zan taba mantawa ba, lokacin da ina siyar da katin waya a cikin jami'ar bayero da ke kano ina ganin yan sin lokacin ake gayamin Hausa suke koya nayi mamaki nake cewar yanzu ya za'ayi yan sin su iya yaranmu na hausa ganin ko films dinsu kake kallo baka gane me suke cewa nace Allah ya kyauta.
Fatana da wannan gidan shi ne ina rokonsu da su kara ba mu Dama wajen fito da wani sabon shiri wanda zai ringa hadamu tare da ma'aikatanku domin tattaunawa game da irin matsalolin da kasashen mu na Afrika ke ciki sannan duk wata gudunmawa da kuke bukata zan bayar da ita dari bisa dari musamman a bangaran harshena na hausa kuma nakan taba rubuce-rubuce a shafukan jaridun Nijeriya na Hausa.
Tabbas a yanzu ina jin gidan radiyon CRI tana daya daga cikin gidajen rediyon da na fi kauna a duniya ganin yadda ta karramani ta hannyar yi min kyauta, a lokacin da naji an kira ni Post office kano suka kirani a wayata domin bani sakonan da aka turomin daga Chaina wato binnin sin kuma na karba nagode sosai Allah ya kara dankon zumunci tsakanimmu da gidan rediyon.
DAGA ANAS SAMINU JA'EN GIDAN MAKERA JIHAR KANO NIJERIYA.