Hakika taron koli na dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da Africa (FOCAC) da aka kammala a farkon watan nan na Disamba ya kawo dimbin alherai da arziki ga al'ummar nahiyar mu ta Afirka, sakamakon shirin gwamnatin kasar Sin na gabatar da muhimman matakan hadin gwiwa 10 da suka taimaka wajen daga likkafar dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka, da ya hadar da batun kiwon lafiya, bunkasa harkar gona, da masana'antu, da sauransu.
Kamar yadda Bahaushe ke cewa, faduwa ce ta zo daidai da zama, domin yayin da tattalin arzikin kasar Sin ya tsaya da kafarsa kuma shugabannin kasar ke da ra'ayin tallafa wa kasashe marasa karfi musamman na nahiyar Afirka, kasar Sin ta gabatar da shirin ta a bayyane na taimaka wa ci gaban kasashen Afirka da ke cikin yanayin fadi tashin raya tattalin arzikin su da samar da ababen more rayuwa da tallafin makudan kudi da suka kai dalar Amurka biliyan 60. Babu shakka, kasar Sin ta nuna jarumtaka wajen fitar da tsabar kudi haka a dadidai lokacin da ake fuskantar mawuyacin halin tattalin arziki, haka nan ta nuna kauna ga al'ummar nahiyar Afirka a kan gabar da suke bukatar haka.
Abin da ya fi burge ni a wannan gaba shi ne, bisa manufar manyan matakan bunkasa hadin gwiwa 10 da kasar Sin ta zartar, kasashen Afirka za su ci gajiyar samun ababen morewa rayuwa da suke matukar bukata, da habaka ayyukan gona, da bunkasa harkar masana'antu, zuba jari da hada hadar kudi, raya al'adu da kyautata yanayin tsaro da sauransu. Lalle za a iya cewa, kasar Sin ta dauki gabarar share wa kasashen Afirka hawaye dangane da matsalolin da suka dade suna ci musu tuwo kwarya.
Dangane da haka, ina jinjinawa kasar Sin bisa wannan tallafi kuma ina fatan dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu za ta ci gaba habaka sannu sannu zuwa wani matsayi na koli.
Mai sauraron ku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners' Club
Kanon Dabo, Nigeria