Wannan dangantakar ta samu tagomashi da habbaka a lokacin Gwamnatin kwaminis ta Mao Zedong cikin karni na 21 (21st Century), daga nanfa likafa tayi gaba wajen kyautatuwar hulda tsakanin Kasar Sin da Afrika, misali gina layin dogo (jirgin kasa), gina masaku, gina titina, samar da ilmi ga juna, harkar lafiya, gona, da sauransu. dalilin hakane Kasar Sin taga ya dace ta kara inganta huldar ta da kasashen Afrika saboda dukkansu Kasashene masu tasowa, kuma al'adunsu kusan daya. Wannan ya basu kwarin gwiwa suka kafa wani Zauren hadakar Sin da Afrika (Forum on China-Africa Cooperation-"FOCAC") wanda ya fara zaman sa na farko a watan Oktoba na 2000 a birnin Beijing. Dan bunkasa tattalin arzikinsu da al'adunsu ta amfanar da juna.Kuma wannan zaure ya kawo cigaba da fahimtar juna sosai.
Kayan da Afrika ke samar ma kasar Sin, sune kamar haka, ta fannin kayan gona akwai auduga daga kasashen Mali, Burkina Faso, Benin da sauransu, Koko daga Ivory coast, danyen man fetur daga Nigeria da sauransu. Cikin abubuwan da Kasar Sin ke samar ma Africa sun hada da tufafi irin namu na gargajiya da kuma suka dace da al'adunmu irinsu Shadda, atamfa, yadin siliki, riguna, darduma, zannuwan gado da sauransu, akwai kuma kayan na'urorin lantarki da suka hada da wayoyin hannu, TV, rediyo, tauraron dan adam (satellites,) sai kuma babura, matoci, kekuna da sauransu.
Sin ta taimaka ma Afrika bangaren gina madatsun ruwa dan aikin noman rani da kuma samar da wutar lantarki, ta hanyar kamfanoninsu irinsu Sinohydro, Chinese Generation Company (CGC), China National water Resources & Hydropower Engineering Cooperation (CWHEC) da sauransu. Kamfanonin sun taimaka wajen gina madatsun ruwa irinsu Lower Kafue George Dam( Zambia), Tekeze, and Amerti-Neshe dam(Ethiopia). Sin na samar da taimako ta bangaren sha'anini tsaro a nahiyarmu ta Africa, wanda ya kunshi horas da da karun soji da kuma kayan aiki, Bangaren ilmi ma ba'a barsu a baya ba, Sin ta taka rawar ganin bunkasa shi, ta hanyar samar da tallafi da kuma kafa makarantu. Misali a Nigeria sun gina Confucius institute a jami'ar Lagos tare da Kano-China bilingual College a Kano, sai kuma a can Kasar Sin akwai Jami'oinsu da ke koyar da harsunan Africa musamman yaren Hausa wanda hakan yayi tasiri wajen kara fahimtar rayuwar mutanen Africa da Sinawa.
Bayan haka in muka duba za muga a janhuriyyar Nijar Kasar Sin ita ta fara hako masu danyen man fetur a yankin tabkin kogin Chad da kuma kafa masu matatar mai a Zinder, wannan nasarar ta jawo bunkasar tattalin arzukin Nijar da kuma samar masu abubuwan more rayuwa da aikinyi. idan muka duba a shekarun baya kasarmu Nijeriya ta samu nasarar harba tauraron dan'adam a sararin samaniya wanda Kasar Sin ce ta kera mana kuma yayi tasiri. Zan tsaya anan, wannan kadan ke nan daga alfanun da muka samu dangane da kulla dangantaka tsakanin Kasar Sin da Africa. Allah Ya kara kyautatawa Amin.
Sani Rabiu.
PO Box 157 Daura
Katsina State
Nigeria