A ranar talata 15 ga watan Satumba, 2015, voa Hausa suka bada labarin cewa, gwamnatin kasar Sin tana yin matsin lamba da takura wa 'yan kabilar Ughuir har ma suna yin kaura zuwa wasu kasashe. Mu dai, mun yi watsi da wannan labari marar tushe. Har kullum, burin kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen kare martaba da kimar dukkan al'ummar kasar Sin baki daya ba tare da yin shishshigi ga lamuransu ba. A shekarar bara ma, wasu kafufin yada labaru na kasashen yammacin duniya da Amurka suka dunga yayata labaru da rahotanni marasa tushe inda suke cewa, gwamnatin kasar Sin sun hana musulmai 'yan kabilar Ughuir a jihar Xinjiang gudanar da azumi a watan Ramadan da ya gabata shekaru 2 ke nan.
A zahirin gaskiya, kasar Sin ta tsaya tsayin daka sosai wajen kin tsoma baki ga harkokin wasu kasashe, Sin tana yin adawa da katsalandan ga lamuran wasu kasashe. Sin ta nace kai da fata wajen sa kaimi ga daukan matakan samun bunkasuwa cikin lumana tare da kokarin kara daukan matakan kara bude kofa ga kasashen waje bisa tsarin yin kyaskwarima bisa manyan tsare-tsare. Lokaci ya yi, kafufin yada labaru na yammacin duniya da Amurka da su daina yin zagon kasa ga tagomashin kasar Sin a fadin duniya, ganin cewa gwamnatin kasar Sin sun dukufa ga manufar samun bunkasuwa tare da ingiza zaman lafiya a duk duniya.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.