Barkanku da warhaka, da fatan kuna cikin koshin lafiya kamar yadda muke a nan birnin Abuja ta Najeriya.
Kamar yadda kuka sani, na fara sauraren nagartattun shirye-shirye da yin mu'amala da sashen Hausa na Gidan Rediyon kasar Sin (CRI) a karshen shekar 1987. Kuma ina iya cewa, a tsawon shekarun da na dauka ina sauraren ku na samu karin ilimi da fahimta sosai game da kasar Sin, da Sinawa da ma kyawawan al'adun Sinawa.
Bugu da kari, ina iya cewa, 'tsakanina da CRI Hausa tamkar kashi ne da tsoka' domin kamar muna manne ne da juna tun da akwai kyakkyawar alaka da fahimta a shekarun nan da muke tare.
A nan, zan so in tunatar da mu cewa, sashen Hausan CRI, wani sashe ne mai matukar muhimmanci wanda ke bayar da gudunmuwa sosai wajen fadakarwa da kara fahimtar da masu sauraren sashen a fadin Duniya, sannan kuma sashen yana taimakawa wajen bayyana wa Duniya zahirin abubuwan da ke faruwa a kasar Sin da Nahiyar Asiya baki dayanta ba tare da gajiyawa ba.
Haka kuma, duk Sinawa da sauran 'yan kasashen waje da ke aiki a sashen, su ma suna bayar da himma da kwazo ainun wajen samar da kyawawan yanayi domin ilmantarwa da fahimtar da masu sauraren a sassa daban-daban na Duniya.
Kuma bayan ta rediyo, sashen na yin amfani da yanar gizo da mujallar 'Zumunta' domin fadakar da Duniya. Godiya ta musamman ga sashen Hausa.
A sakamakon gasar kacici-kacici da sashen Hausa ya shirya don masu saurare, na samu dama har sau biyu na kai ziyara zuwa kasar Sin; karo na farko a shekara ta 2001, karo na biyu kuma a shekara ta 2012.
A nan, ina so in tunatar da mu cewar, bayan dawowa na Najeriya a 2012, na rubuta bayanai dalla-dalla masu kyau bisa ga abubuwan da na gani a kasar Sin, har kuma jaridar Hausa mai suna 'Aminiya' a nan Abuja ta wallafa.
Saboda haka, a nan zan yi murna kwarai idan na samu wata damar don sake kai ziyara kasar Sin karo na uku domin in karasa bayyana wa 'yan Najeriya abubuwan jin dadi da na fara rubutawa a 2012 din.
A hakikanin gaskiya, ina bege kuma ba zan manta da irin karimci da yakana ba da Sinawa suka nuna mana; ga abinci mai dadin dandano, ga abubuwan more rayuwa, ga kyawawan al'adu na kanana da manyan kabilun kasar, ga wuraren yawon bude idanu da shakatawa da kara ilimi, ga dabbobi iri-iri, ga dazuzzuka da kayayyakin tarihi domin kada a manta baya, ga abubuwa nan iri-iri wadanda babu adadi.
A karshe, ina so in yi amfani da wannan dama ta yau domin aika gaisuwa ta musamman gare ku, da kuma kara sanar da ku cewar, 'ina alfahari da CRI Hausa da ma CRI baki dayanta a kullum, kuma bana yin dana-sani ko kadan da yin mu'amala da ku'.
Ina yi muku fatan alheri a kullum. Sai na sake ji daga gare ku, Allah Ya kara zumunci, xie xie.
Naku,
Salisu Muhammad Dawanau
30 ga Yuli, 2015