in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dalai Lama babban mai laifi ne bisa aniyarsa ta aiyana yancin kan Jihar Tibet ta kasar Sin
2015-07-16 15:21:28 cri

Ya kyau, mahukuntan kasar Amurka su daina yi wa kasar Sin shishshigi da katsalandan a lamuranta na siyasar cikin gida, masamman ma yadda jami'an Amurka ke kokarin wuce gona da iri adangane da batun Dalai Lama da kuma jihar Tibet ta kasar Sin. Muddun mahukuntan kasar Amurka suka nuna amuncewarsu da batun yancin jihar Tibet kamar yadda bujirarren madugun yan a-waren jihar Tibet Dalai Lama ya sha fadi, toh ko shakkan babu yin hakan na da muguwar illa ga dangantar diplomasiyyar dake akwai tsakanin mahukuntan Beijing da na Washington Dc. Kamata ya yi dukkan jawaban da wakilan Amurka za su tattauna yayin liyafar taya Dalai Lama murnar zagayowar ranar haifuwarsa inda kuma yake cika shekaru 80 duniya a ranar juma'a mai zuwa su kasance wasu batutuwa ne na daban, ba wai batun yancin kan jihar Tibet ta kasar Sin ba. A zahirin gaskiya dai, Dalai Lama bajirarre ne wanda ya yi kokarin haifar wa kasar Sin da jama'arta baraka inda ya aiyana yancin kan jihar Tibet mai cin gashin kanta. Dud duniya sun amunce da cewa, jihar Tibet mai kewaye da tsaunika kuma jiha mai cin gashin kanta, wani bangare ne na kasar Sin kuma ba abune da gwamnatin kasar Sin za su amunce da shi ba. Dan haka, kuskure ne babba ga gwamnatin Amurka na su nuna gamsuwarsu da batun ballewar jihar Tibet daga kasar Sin kamar yadda Dalai Lama mai gudun hijira a kasar Amurka ya sha nanatawa.

Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China