Tare da fatan baki dayan ma'aikatan sashen Hausa suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing, bayan haka, ina farin cikin sanar da ku cewa na samu sauraren sabon shirin ku na 'Sin da Afirka' na jiya Talata 30 ga watan Yuni, inda malam Bako Li ya zanta da wasu Hausawa mazauna kasar Sin dangane da batun nan na shafawa kasar Sin kashin kaji da cewa, wai an hana Musulmin kasar Sin gudanar da ibadar Azumi.
Hakika, wannan hira ta yi ma'ana sosai saboda yadda malam Tukur Tinglin ya fito fili ya karyata duk wata jita-jita kan cewa, wai an hana Musulmi Sinawa yin Azumi, kamar yadda malam Babangida wani dalibi dake karatu a lardin Hunan shi ma ya kara jaddada gaskiyar lamari cewa, baki dayan Sinawa a fadin kasar Sin suna fara idabar Azumi kamar sauran al'ummar Musulmi a duk fadin duniya. Ba shakka, wasu kafafen yada labari su kan yi amfani salon farfaganda don bata wa kasar Sin suna a idon duniya. Lallai wannan bai dace manufofin da kasar Sin ke bi na zaman tare cikin lumana ba.
Ina son yin amfani da wannan dama wajen jan hankalin ma'abota dandalin nan na sada zumunta wato facebook, da su rika yin nazarin duk wani labari da wani ya dora a shafin domin tantance sahihancinsa. Hakan yana da muhimmancin gaske wajen gujewa yada labaran karya marasa tushe balle makama. Wannan shawara ta biyo bayan yin la'akari da yadda wasu bata gari ke amfani da farin jinin da shafin sada zumunta na facebook ke da shi wajen yada jita-jita da labaran batanci ga wasu. Da fatan za a rika kiyayewa da tushen kowanne labari kafin amincewa ko yada shi ga sauran al'umma.
Mai sauraron ku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners' Club
Kanon Dabo, Nigeria