in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Labaran hidimar Azumi a Xinjiang da Kano cikin hotuna ya burge ni
2015-07-08 09:10:46 cri
Zuwa ga sashen Hausa na Rediyon kasar Sin.

Bayan gaisuwa mai yawa tare da fatan alheri ga ma'aikatan ku baki daya, ina fatan kuna lafiya a birnin Beijing kamar yadda nake lafiya. Hakika, na samu dubawa tare da yin nazarin jerin hotunan hidima da sauran ayuukan ibadah da al'ummar Musulmi ke gabatarwa yayin watan Azumi na bana da ke shirin karewa. Kuma na yi la'akari da irin kamanceceniya dake tsakanin ayyukan Azumi a jihar Xinjiang da kuma nan jihar Kano, inda na fahimci ba bu wani bambanci sai na lokacin yin sahur da kuma bude baki.

Abin da ya fi burge ni da hotunan shi ne, yadda al'ummar Musulmi ke ci gaba da gudanar da harkokin su na yau da kullum a Xinjiang yayin da suke gudanar da ibadar Azumi, musamman yadda Musulmin Xinjiang suke ba da muhimmanci wajen cin abincin bude baki tare da abokai da sauran iyali. Ba shakka, wannan ya yi kamanceceniya da yadda al'amarin ke tafiya a kasar Hausa cikin iyali yayin gudanar da ibadar watan Azumi, inda iyalai da dama kan gayyaci abokan arziki don cin abincin bude baki tare cikin farin ciki. Wani abu da na dada yin la'akari da shi bisa nazartar wadannan hotunan na Xinjiang da Kano shi ne, akwai kamanceceniya mai yawa tsakanin yanayin abincin bude baki a garuruwan biyu wajen ba da muhimmanci ga kayan marmari da sauran 'ya'yan itatuwa.

A ra'ayi na, bambancin ibadar Azumi a garuruwan Xinjiang da Kano shi ne lokaci, yayin da ake cin abincin Sahur da karfe 5:50am, a Nijeriya a na cin abincin Sahur ne da misalin karfe 4:45am. Kazalika, a na yin bude baki a jihar Xinjiang da misalin karfe 10:00pm na yamma, amma a Nijeriya tun da misalin karfe 6:55pm a ke shan ruwa. Wato tsahon lokacin yin Azumi a kowanne yini a Nijeriya ya kai kimanin sa'oi 13 da 'yan mintuna, yayin da a jihar Xinjiang ya kai kimanin sa'oi 16 da 'yan mintuna.

Mai sauraron ku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Great Wall CRI Listeners' Club

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China