Dud da cewar, mahalarta taron kasashen Brics na kasar Rasha sun samu zarafin sauraren jawaban shugabannin kasashen Brics su 5, kuma jawabin da suka gabatar mai karko ne kuma yana da alfanu ga samun bunkasuwar kasashen Brics, amma dai, ni nafi gamsuwa da jawabin da shehun malami kuma shugaban kasar Sin mr. Xi Jinping ya gabatar a zauren taron kasashen Brics a kasar Rasha. A cikin jawabinsa, shugaban kasar Sin mr. Xi Jingping ya ce, ''akwai bukatar kasashen Brics su daura muhimmanci ga kara bunkasa hadin gwiwa a tsakaninsu ta hanyar kara bunkasa tattalin arzikin kasashensu da zuba jari da kara hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakaninsu kana kamfanoni da masana'antun kasashen Brics su kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu ta yadda za su samu bunkasuwa mai daurewa.
Daga Malam Ali Buuge Gashua.