in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Na gamsu da jagorancin mr. Xi da jks a kasar Sin
2015-07-12 12:25:40 cri
Babu shakka, kowace al'umma tana da bukatar samun shugaba haziki mai tunani da hangen nesa kuma mai kaunar ci gaban kasa da al'ummarta, kamar yadda har kullum shugaban kasar Sin Mr. Xi Jinping ke bada misali. Daga shekarar 2013 zuwa yanzu 2015, kasar Sin da al'ummarta sun shiga wani saban mataki na samun ci gaba masu yawa sosai. A zamaninsa mr. Xi Jinping shugaban kasar Sin, al'ummar kasar Sin sun gamsu bisa kyakkyawan jagorancinsa inda kasar Sin ta kai wani mataki na koli wajen samun habakar tattalin arziki da kuma samun manyan nasarori a yakin da gwamnatin kasar Sin ke yi warjanjan da cin hanci da karbar rashawa a kasar Sin. Bisa dagewa, shugaban kasar Sin mr. Xi da jam'iyarsa ta kwaminis sun yi nasarar daura kasar Sin da al'ummarta bisa nagartattun manufofi bisa zaman karko da lumana da kuma nuna kishin kasa da al'ummarta. Daga shekarar 2013 zuwa 2015, kasar Sin da jama'arta sinawa sun kara samun martaba da kima da tagomashi a dud duniya baki. Ya kyautu, sauran shugabannin kasashen duniya su hanzarta yin koyi da shugaban kasar Sin mr. Xi Jinping bisa kyakkyawar aniya da manufofin kishin kasa da al'ummarta da shugaban kasar Sin ke da shi.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China