Ina mai mika sakon jaje da alhini da ta'azziya ga iyalai da 'yan uwan mutanen da suka rasu a sa'ilin da wata girgizar kasa mai karfin maki 6.5 na ma'aunin girgizar kasa(magnitude) ta abka wa Jihar Xinjiang dake sashin arewa maso yammacin kasar Sin. Haka nan, muna yaba wa jami'an aikin ceton gaggawa na kasar Sin bisa hanzarta kai dauki da aiwatar da aikin ceto da suka yi a yankunan da bala'in girgizar kasa ta ritsa da su a jihar Xinjiang.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.