in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin: A gani na
2015-06-19 15:32:13 cri
Sanin kowa ne, kowace kasa da al'umma a Duniya tana da irin baiwa da Ubangiji Ya yi mata. Wasu an yi musu baiwar kiba da farar fata, wasu an yi musu baiwar gajarta, wasu kuwa dogaye ne ainun.

A nan, ina so ne zan yi tsokaci ne a takaice bisa ga muhimmancin baiwar da aka yi wa kasar Sin na yawan al'umma. Hakika, ba sai mun yi ta maimaita wannan baiwa ba amma dai abin da nake so in ce shi ne, baiwar yawan al'umma abu ne mai kyau sosai, ko babu komai, sai an yi da ku a harkokin Duniya masu dumbin yawa.

A sanadin baiwar al'ummar kasar Sin, a cikin jama'ar Sinawa, akwai masana masu yawan gaske a bangarori masu dama, kuma wadannan masana dole ne a nemi agajin su musamman na bayar da gudunmuwa a fannonin kiwon lafiya da kimiyya da fasaha da kasuwanci da noma irin na zamani da dai sauransu. Ashe kenan baiwar al'umma abu ne mai matukar kyau.

Koda yake wasu masana sun sanar cewa bai dace ba idan kasa ta kasance mai yawan al'umma, amma dai a nawa tunanin bai kamata a yi irin wannan hasashe ba, saboda yawan al'umma dai na Ubangiji ne. Sannan kuma, yana daga cikin abu mai kyau idan kasa ta samu shugabanci na kwarai musamman mai yawan al'umma wajen aiwatarwa ko gudanar da ayyukan ci gaba da kuma kasancewa akwai kishin kasa a zuciya.

A gani na, duk kuwa da yawan al'ummar kasar Sin, akwai kyakkyawan shugabanci, kuma babu yunwa. Kuma, abubuwa da dama suna tafiya kamar yadda ya kamata, babu kakkautawa, domin kyautata wa al'umma.

Ashe kenan, muna iya cewa, ya kamata sauran kasashen Duniya, wadanda basu son yawan al'umma, su rika yin koyi da kasar Sin domin gano hanyoyin da zasu bi domin bunkasar al'ummomin su a dukkan fannoni.

Hakika, muna yi wa kasar Sin kyakkyawan zato wajen yadda take taimaka wa wasu kasashen Duniya. Sannan kuma, muna yaba mata bisa ga yadda take tafiyar da al'amuranta domin kara kyautata mu'amalarta da sauran kasashe. Haka kuma, muna yaba mata bisa ga yadda take kirkiro nagartattun dabaru wajen inganta karfin tattalin arzikinta wadda ya zama abin koyi a kullum.

Ba zan manta da kokarin ku a sashen Hausa ba, musamman wajen fadakarwa da fahimtar da masu sauraro bisa ga karfin kasar Sin a fannoni masu yawa. Fatan alheri ga kasar Sin, da Sinawa a duk inda suke a fadin Duniya.

Naku,

Salisu Muhammad Dawanau

Labarai masu Nasaba
Ga wasu
v Watan Ramada (azumi) ya kama 2015-06-14 12:13:43
v Ra'ayin mai sauraro 2015-06-11 09:32:13
v Barka da warhaka! 2015-06-09 08:40:28
v Ranar kare muhalli ta duniya 2015-06-06 16:31:28
v Sanarwar daurin aure 2015-06-05 15:10:39
v Sakon jaje kan hadarin jirgin ruwa a Sin 2015-06-03 14:52:32
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China