Gidan Cinema tambar wani guri ne na shakatawa ga mutane masu zuwa kwallo dan samun wadatar jin dadi da kuma shakatawa a cikin tarin jama'a. Tsokacin da malamai Mamman Ada da Lubabatu suka yi a sa'ilin da suke gabatar da shirin ''Allah daya gari Bambam''. Agaskiya jin labarin cewa, wasu gungun dalibai masu bada aikin sa-kai na masammam wajen kawo makafi gidan Cinema dan samar da jin dadi ga rayuwar makafi har ma ga shi an ce, akwai irin wannan Cinema guda 17 a duk fadin kasar Sin. Toh, yanzu dai muna iya cewa, makafi a kasar Sin suna samun kulawa da tallafi na masamman inda su ma makafin suke iya samun zarafin zuwa Cinema dan samun yallawar jin dadi kuma hakan wani muhimmin yanci ne na masamman ga rayuwar makafi a kasar Sin kuma dud da cewar su makafi suna da nakasar rashin gani a rayuwarsu, amma dai su ma suna iya samun damar shiga Cinema su ji dadi inda suke samun karin bayani daga dalibai masu aikin sa-kai adangane da abunda suka ji a cikin Cineman. Mu ma a taraiyar Nigeria da sauran kasashenmu na Afirka masu tasowa muna fata wata rana dalibai yan makaranta za su yi koyi da takwarorinsu na kasar Sin wajen tallafa wa makafi inda suke kai su gidan Cinema dan ba wa su makafin damar samun watayawa da shakatawa a rayuwarsu ta yau da kullum.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.