in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Filin 'Kiwon Lafiya'
2015-06-19 15:35:45 cri
Ko shakka babu, kankana da sauran nau'ukan 'ya'yan itatuwa suna daga cikin abubuwa masu taimaka wa jikin dan Adam, wasu wajen gina jiki mai lafiya, wasu kuwa wajen samar da kariya ga kamuwa daga kananan cututtuka.

Shirin ku na ranar 16 ga Yuni zai taimaka sosai wajen fadakarwa ga musamman wadanda ke son kankana da sauran 'ya'yan itatuwa. Sannan, duk wanda ya saurari shirin, na tabbata ya samu karin ilimi ta yadda zai sarrafa kankana, da kuma samun wani ilimin ta yadda za a kauce daga kamuwa daga cututtuka ta bin hanyoyin da ku ka zayyana a shirin.

Bugu da kari, a shirin, kun kawo batun tsafta wadda wani abu ne da kowa yake na'am da shi. Shaftace kankana da wuraren da za a dafa abinci, da muhimmancin yin hakan a rayuwar dan Adam.

Muna godiya ga wannan shiri, da fatan Allah Ya kara muku basira wajen bin hanyoyin da suka dace domin binciko bayanai masu ma'ana, don ceto rayuwa.

Ku huta lafiya.

Salisu Muhammad Dawanau

Labarai masu Nasaba
Ga wasu
v Kasar Sin: A gani na 2015-06-19 15:32:13
v Watan Ramada (azumi) ya kama 2015-06-14 12:13:43
v Ra'ayin mai sauraro 2015-06-11 09:32:13
v Barka da warhaka! 2015-06-09 08:40:28
v Ranar kare muhalli ta duniya 2015-06-06 16:31:28
v Sanarwar daurin aure 2015-06-05 15:10:39
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China