in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabuwar dokar hana shan taba ta dace
2015-06-19 15:38:02 cri
Zuwa ga sashen Hausa na CRI.

Bayan gaisuwa mai yawa tare da fatan alheri gare ku, da fatan duk kuna cikin koshin lafiya a birnin Beijing kamar yadda na ke lafiya. Bayan haka, ina farin cikin sanar da ku cewa, na samu sauraron sabon shirin ku na 'Allah daya gari bamban' a jiya Laraba 17 ga wata, inda malamai Ibrahim Yaya, Maman Ada da kuma Saminu Alhassan suka gabatar mana da tattaunawa mai ilimantarwar gaske dangane da sabuwar dokar hana shan taba sigari a wuraren da jama'a ke zama a birnin Beijing da sauran biranen kasar Sin.

Hakika, wannan doka ta dace matuka idan aka yi la'akari da cewa, akwai miliyoyin Sinawa dake da dabi'ar zukar taba sigari a kowacce rana ba tare da yin la'akari da illar da hakan ke yi ga lafiyar su ba da kuma ta sauran al'umma. Koda yake, an tanadar da wasu wurare na daban da masu shan tabar ka iya kebewa don su sha tabar, amma duk da haka, ina fatan hukumomi ba za su taba gajiyawa ba wajen ci ga da fadakar da al'umma illar da ke tattare da zukar taba sigari.

Wani abu da ya fi jan hankali na dangane da wanna sabuwar dokar shan taba shi ne, yadda dokar ta shafi magidanta dake da dabi'ar shan tabar a gidajensu, lamarin da ke cutar da iyali baki daya ta fuskar lafiya. Wato yanzu, magidanta ba su da ikon zukar taba sigari a gidajensu, dole sai dai su fice zuwa wasu wurare na daban da aka tanada domin shan tabar. Wannan shakka babu, zai ba da gudunmawa sosai wajen rage yawan karan sigari da kowanne mutum ke iya sha a kowacce rana. Da fatan, hukumomi ba wai a kasar Sin ba, har ma da sauran kasashen duniya za su ci gaba da bibiyar manufofin da za su dakile dabi'ar shan taba.

Mai sauraronku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Great Wall CRI Listeners' Club

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ga wasu
v Filin 'Kiwon Lafiya' 2015-06-19 15:35:45
v Kasar Sin: A gani na 2015-06-19 15:32:13
v Watan Ramada (azumi) ya kama 2015-06-14 12:13:43
v Ra'ayin mai sauraro 2015-06-11 09:32:13
v Barka da warhaka! 2015-06-09 08:40:28
v Ranar kare muhalli ta duniya 2015-06-06 16:31:28
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China