Kasashen Sin da taraiyar Nigeria sun kulla huldar jakadanci bisa diplomasiyya da hadin gwiwa da musayar al'adu kuma sannu a hankali kasashen 2 suna kara kyautata zumunci da abokantaka dake wanzuwa a tsakaninsu bisa lumana da amuncewa juna. A ranar asabar 16 ga watan May Shekara ta 2015, wakilin cri Hausa dake birnin Abuja, Nigeria malam Murtala Zhang ya bada rahotan cewa, jakadan kasar Sin dake birnin Abuja ya mika tallafin kyautar motocin jigilar marasa lafiya guda 12 ga gwamnatin taraiyar Nigeria dan bada taimako ga sashin kula da lafiya na kasar dan bunkasa aiyukan bada jinya ga asibitocin Nigeria. Hakika wannan tallafi da kasar Sin suka mika wa gwamnatin Nigeria ta hannun jakadan kasar Sin dake Nigeria, ya alamunta kyakkyawar aniyar kasar Sin ta bunkasa sha'anin kiwon lafiyar jama'ar taraiyar Nigeria. Yau fiye da shekaru 40 da kafa huldar diplomasiyya da cinikaiya da musayar al'adu da hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare kuma kasar Sin da taraiyar Nigeria sun samu ci gaba mai yawa sosai, fatanmu har kullum shine, kasar Sin da taraiyar Nigeria su kara fadada huldar amunci dake tsakaninsu ta yadda kasashen 2 za su kara bude wani saban babi na kara hadin gwiwa da juna cikin lumana bisa yardar juna.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua, shugaban cri Hausa listener's club na jihar Yobe, Nigeria.