Ina fata kuna lafiya. Fatan alheri a gare ku kullum.
A ayyukan CRI Hausa, kadan daga dalilan da yasa ku kan burge ni da sauran masu sauraro shi ne yadda ku kan kawo mana labarai da muhimman bayanai a kan lokaci, kuma da dumi-duminsu.
Ba zan manta ba, a lokutan zabukan da muka gudanar a nan Najeriya kwanakin baya, kun kawo mana gamsassun rahotanni masu nasaba da zabukan. Muna yaba muku sosai a bias wannan kokari.
A karshen makon da ya gabata, yayin ziyarar Jakadan kasar Sin a nan Najeriya zuwa jihar Kano, da taimakon wakilinku malam Murtala, mun samu duk kan bayanai masu nasaba da wannan muhimmin ziyara mai dauke da tarihi.
Bugu da kari, wakilin naku ya kawo mana wasu kyawawan bayanai game da ziyararsa ta farko a jihar, yayin da ya zagaya cikin birnin Kano domin kawo mana rahotanni da kuma abubuwan da ya gani da idanunsa a birnin.
Ga wadanda basu san birnin Kano ba, na san sun samu karuwar ilimi a rahotannin zagayen na malam Murtala. Gaisuwa ta musamman gare ku da wannan kokari.
Ku huta lafiya.
Salisu Muhammad Dawanau