Yayinda wata sabuwar girgizar kasa ta kara abka wa gabashin kasar Nepal a ranar talata 12 ga watan May-2015 inda akalla mutane 40 suka hallaka. A kasar Sin kuma, rana ce ta bikin cikon shekaru 7 da abkuwar girgizar kasa a lardin Sichuan inda akalla sinawa 87,000 suka rasu a wancan lokacin wato, 2008-2015. Wannan biki na tunawa da dubban sinawa da suka rasu a lardin Sichuan da gwamnatin kasar Sin suka aiyana, ya alamunta halin dattaku da tausayi da shugabannin kasar Sin karkashin jagorancin mr. Xi Jinping suke da shi. Babu shakka wannan muhimmiyar rana ce ga iyalai da yan uwan dubban sinawan da suka rasa rayukansu a sanadiyyar girgiza a lardin Sichuan na kasar Sin a kimanin shekaru 7 da suka gabata. Ware ranar 12 ga watan May a matsayin ranar cikon shekaru 7 da tunawa da sinawan da suka mutu a lardin Sichuan, agaskiya shugabannin kasar Sin ta zamani sun yi dogon tunani da suka aiyana ranar masamman dan tunawa da rasuwar dubban sinawa a lardin Sichuan na kasar Sin. Muna fata kasashen Sin da Nepal za su daina samun abkuwar bala'in girgizar kasa har abada, amin.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.