Babu shakka ziyarar da firaministan harkokin wajen kasar Sin mr. Wang Yi zai fara a ranar 10 zuwa ranar 17 ga watan Janairun 2015 da muke ciki a wasu kasashenmu na Afirka su 5, wani muhimmin mataki ne kasar Sin ta dauka a karon farko a sabuwar shekara ta 2015 dan bude wani saban babi na samun bunkasuwa tare da aminanta kasashenmu na Afirka. A yayin ziyarar firaministan harkokin wajen kasar Sin mr. Wang Yi a kasashenmu na Afirka, mr. Wang Yi zai kai ziyarar amunci a kasashenmu na Afirka su 5 da suka hada da: camaroun, Sudan, Equatorial Gunea, Kenya da Congo Kinshasa. Hakika wannan ziyara da mr. Wang Yi da tawagarsa a kasashenmu na Afirka, ka iya kawo babbar moriya da ci gaba bisa manyan tsare-tsare bisa karko da lumana ga nahiyoyin Sin da Afirka. Sin har kullum tana bin nagartattun matakai na yin hulda da kasashenmu na Afirka dan samun bunkasuwa cikin yakini da lumana, al'amarin da ya sabbaba samun bunkasuwa ga kasashenmu na Afirka masu tasowa. Kasashen Sin da Afirka suna da manufofi da yanayi guda na samun bunkasuwa tare da juna, dan haka muna maraba da ziyarar sada zumunci mai cike da tarishi da firaministan harkokin wajen kasar Sin mr. Wang Yi da tawagarsa zasu kai zuwa nahiyarmu ta Afirka a ranar 10 zuwa 17 ga watan Janairu 2015. A cikin shekaru fiye da 50 da kasashenmu na Afirka masu tasowa suka kafa huldar diplomasiyya da cinikaiya da musayar al'adu da sabuwar kasar Sin ta zamani, Afirka da Sin sun samu babban ci gaba mai yawa a tsakaninsu.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.