Bayan gaisuwa mai yawa da fatan alheri, ina fatan baki dayan ma'aikatan sashen Hausa suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing. Bayan haka, na rubuto wannan sako na musamman ne domin gabatar da sakon jaje ga al'ummar Sinawa dangane da bala'in rasuwar mutane fiye da talatin a birnin Shanghai sakamakon turmutsutsun jama'a da ya faru lokacin da jama'a ke tsaka da gudanar da bikin maraba da shigowar sabuwar shekara ta 2015 a birnin na Shanghai.
Da fatan iyalan da wannan bala'i ya shafa za su dauki hakurin jure rashin da suka yi, kuma da fatan wadanda suka samu raunuka za su samu sauki cikin sauri. Tare da fatan ba za a sake samun aukuwar bala'i mai kama da wannan ba a kasar ta Sin da ma duniya baki daya.
Mai sauraronku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners' Club
Kanon Dabo, Nigeria