Bayan gaisuwa mai yawa tare da fatan alheri ga baki dayan ma'aikatan sashen Hausa da ke birnin Beijing. Bayan haka, ina farin cikin shaida muku cewa na kalli daya bayan daya shirin musamman na hoton bidiyo mai taken 'Kwadon Baka' da ku ka sanya kan shafin ku na yanar gizo. Hakika, wannan shirin bidiyo ya kayatar da ni matuka saboda a cewar dan Hausa, gani ya kori ji. Domin wannan shirin bidiyo tamkar wani yawon shakatawa ne ta hanyar yanar gizo, sakamakon hotunan bidiyo na gidajen cin abincin halal na Musulmi da ke biranen Beijing da Xian wanda mai kallo zai iya kashe kwarkwatar idanunsa.
Kodayake, faya fayen bidiyon sun taimaka min sosai wajen fahimtar irin yadda ake shirya abincin halal a kasar Sin, abin dai kamar da wuya domin bayan kayan hadin abincin da suka sha bamban da na Hausa, hatta da kayan girkin da ake amfani da su wajen sarrafa abincin ba bu irin su a kasar Hausa. Amma duk da wannan bambance bambance bai hana ni fahimtar dadi da kuma sirrin dake cikin girke girken abincin halal na kasar Sin ba. Idan ba zan tsawaita magan ba, daga cikin abincin halal da ya hadar da Guantang Baozi da Yangrou Paomo da turararren naman rago, da farfesun kayan cikin rago har ma da tsiren naman na rago, gaskiya duk na fi sha'awar Dapanji. Saboda wannan abinci da gani zai yi dadi saboda ya hada kayan dadi masu dadi, gina jiki da kuma kara lafiya. Dapanji ya yi kama da faten dankali na kasar Hausa amma kuma ya fi shi kayan hadi masu daraja da amfani ga dan Adam.
Kodayake na taba cin Yangrou Paomo yayin ziyarar mu a birnin Xi'an, amma duk da haka na fi kwadayin Dapanji, kuma ina shawartar duk wani Bahaushe da ya samu zarafin ziyara a kasar Sin to ya jarraba abincin halal mai suna Dapanji.
Godiya ta musamman ga malamai kamar su Lubabatu (Lei) da Bilkisu (Xin) da Kande (Gao) da kuma Amina (Xu) bisa gudunmawar da suka bayar ga Fatimah I. Jibril wajen hada wannan shiri na musamman.
A karshe, ina son amfani da wannan dama wajen mika sakon gaisuwa ta na sabuwar shekara 2015 ga baki dayan ma'aikatan sashen Hausa na CRI da masu sauraron sa a fadin duniya.
Mai sauraron ku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners' Club
Kanon Dabo, Nigeria