Babu shakka, gudanar da bikin tunawa da kisan gillar da Sojojin kasar Japan suka aiwatar akan al'ummar sinawa a birnin Nanjing da gwamnatin kasar Sin ta fara a karon farko, muhimmin batu ne da har abada al'ummar kasar Sin da masoya kasar Sinawa ba za su taba mantawa da shi ba a rayuwarsu. Kisan dubban sinawa a birnin Nanjing tare da cin zarafin mata Sinawa inda sojan Japan suka yi wa Sinawa mata fyade babban kuskure ne sojojin kasar Japan suka aikata mafi mani a tarishin dan adam a duniya. Kisan sojojin kasar Sin da fararen hula su 300,000 da sojan kasar Japan suka yiwa yankan rago bayan sun mika wuya gare su, ya alamunta karfin tuwo da rashin imani da sojan Janawa suka aikata akan al'ummar sinawa a birnin Nanjing kuma kisan kare-dangi na 2 a duniya bayan kisan kiyashi da aka aikata akan musulmi a Bosniya a shekarar 1993-1995 inda akalla Sojan kasar Yugoslavia suka kashe fararen hula albeniyawa musulmi su 7,000. Ya zama dole, gwamnatin kasar Japan su nemi afuwar laifin da sojojin kasarsu suka aikata akan dubban sinawa a birnin Nanjing a shekarar 1937. Kana ina yaba wa gwamnatin kasar Sin da suka ware ranar masamman dan tunatar da al'ummar sinawa da al'ummomin duniya yadda sojojin Japanawa suka mamaye birnin Nanjing tare da aikata danyen aikin kisan kare-dangi akan sojoji da fararen hula na kasar Sin a shekarar 1937. Ware ranar, zai taimaka sosai wajen kara tunatar da duniya irin barnar rayuka da rashin imani da sojojin mamayar kasar Japan suka aikata a birnin Nanjing. Ya dace, kasa da kasa su la'anci kasar Japan bisa wannan wauta da rashin imani da sojojin Japanawa suka aikata akan dubban sinawa a birnin Nanjing na kasar Sin. Mu ma masu sauraro, muna yin tir da wannan danyen aikin rashin imani da sojojin mamaya na kasar Japan suka aikata akan sinawa a birnin Nanjing.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.