Tare da fatan baki dayan ma'aikatan sashen Hausa suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing, bayan haka, ina farin cikin shaida muku cewa, na saurari sabon shirin ku na 'Gani Ya Kori Ji' na ranar Laraba 10 ga wata, inda Malamai Ibrahim Yaya da Mamman Ada Saminu Alasan suka tattauna dangane da taron kasa da kasa kan sauyin yanayi da aka gudanar birnin Lima na kasar Peru.
Hakika, wannan taro ya yi ma'ana kuma ya zo a daidai wani lokaci da batun sauyin yanayi da gurbatar muhalli ke kara jan hankulan masu fafutuka dangane da muhallin da kuma sauran al'umma baki daya. Koda yake, an riga an gudanar da taruka da yawa kan wannan batu a baya, amma wanda aka gudanar a baya bayan nann a birnin Lima na kasar Peru ya alamanta cewa, har yanzu ba a cimma burin rage fitar da abubuwan da kan jawo gurbacewar muhalli ba. Amma a hannu daya kuma, taron ya bayyana irin muhimmancin da kasashen duniya ke dorawa kan muhalli. Misali, kasar Sin ita kadai ta aika da wakilai har 80 zuwa taron na Lima, wannan wata shaida ce dake nuna irin muhimmancin da kasar Sin ke bayarwa ga batun sauyin yanayi ko gurbatar muhalli. Dangane da haka, ya dace kasashen duniya su yi koyi da kasar Sin wajen bayar da muhimmanci ga tarukan sauyin yanayi domin tabbatar da cewa an magance wannan matsala ta sauyin yanayi.
Ba shakka, kowa ya zama shaida dangane da illoli da sauran matsaloli da sauyiun yanayi ke kawo wa kasashen duniya ta fannoni da dama da suka hada da tattalin arziki da zamantakewa. Don haka, ya dace kasashen duniya su ci gaba da bayar da muhimmanci ga batun sauyin yanayi dake da alaka da kyakkyawar makomar tattalin arzikin duniya da zamantakewa.
Mai sauraronku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners' Club
Kanon Dabo, Nigeria