in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Abincin halal a kasar Sin
2014-12-18 14:51:27 cri
Zuwa ga sashen Hausa na Rediyon kasar Sin.

Bayan dubun gaisuwa tare da fatan alheri ga ma'aikatan sashen Hausa na CRI, ina farin cikin shaida muku cewa na ji dadin sauraron shirin nan naku mai farin jini na 'Allah daya gari bamban' na ranar Jumu'a 12 ga wata, inda jagoran shirin malama Lubabatu tare da Mamman Ada suka gayyaci malama Fatimah Jibril don tattaunawa kan ire-iren abinci na halal a kasar Sin.

Hakika, shirin ya burge ni sosai sakamakon yadda malama Fatimah Jibril ta gabatar da bayanai dalla dalla dangane da gidajen cin abinci na halal a manyan biranen kasar Sin, tare da irin nau'oin abinci na halal da a ke samu a jihohin Musulmi irin su jihar Ningxia da lardin Shaanxi dake da rinjayen al'ummar Musulmi. Ko shakka babu, kalaman malama Fatimah sun bayyana irin zaman walwala da jin dadi da al'ummar Sinawa ke morewa a duk fadin kasar Sin. Sa'an nan labarin wadatuwar gidajen abinci na halal a kasar Sin na alamanta 'yancin gudanar da addini a kasar China. Sabanin yadda wasu ke zargin cewa, wai a na tauye 'yancin bin addinin Musulunci a kasar Sin.

Daga cikin abincin Musulmi da a ka yi bayani a kai, na fi sha'awar naman rago da a ke sarrafa shi ta hanyar turarawa, saboda wannan salon sarrafa naman rago ya zama na daban ga al'ummar Sinawa su kadai. Saboda sauran al'ummar duniya suna dafawa ne ko gasawa ko kuma soyawa. Ina fatan za ku sanya mana wannan hoto na turararren naman rago a shafin ku na yanar gizo.

Ni kaina shaida ne na yawaitar gidajen cin abincin halal a kasar Sin, domin yayin ziyara ta a kasar Sin bisa gayyatar sashen Hausa na CRI a shekarar 2011 na ci abincin halal a gidajen abincin halal daban daban a birnin Beijing da birnin Xi'an hedkwatar lardin Shaanxi.

Mai sauraron ku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Great Wall CRI Listeners' Club

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China