in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shan taba bayan tashi daga barci na kara barazanar kamuwa da sankarar huhu
2015-01-17 20:37:36 cri


Da yawa daga masu shan taba kan sha taba da zarar sun farka daga barcin safe. Har ma wasu daga masu matukar sha'awar shan tabar kan kunna ta kafin su goge hakoransu. Sai dai wani sabon nazarin da aka yi a kasar Amurka game da hakan ya nuna cewa, shan taba bayan tashi daga barci na matukar kara barazanar kamuwa da ciwon kansa, ko sankarar huhu. Kana binciken ya nuna cewa koda ya zamo dole a shan taba, kamata ya yi a sha ta, bayan rabin awa da tashi daga barci.

Masu nazari daga jami'ar jihar Pennsylvania ta Amurka sun gabatar da wani rahoto a kwanan baya, wanda ya kunshi sakamakon tantanci wasu baligai masu shan taba dubu 1 da dari 9 da 45 a duk fadin kasar. Wadanda suka yiwa bincike kan al'adarsu, ciki had da lokacin da a kullum su kan sha taba a karon farko bayan sun tashi daga barci a safiyar ko wace rana. Sakamakon wannan bincike dai ya nuna kimanin sulusin masu sha tabar kan sha ta cikin mintoci 5 kacal da tashin su daga barcin safe, yayin da kimanin sulusi na biyu kan kunna tabar cikin mintoci 6 zuwa rabin awa bayan tashi daga barci. Sai kuma wani kashin kimanin 18 cikin dari, dake shan taba a cikin rabin awa zuwa awa daya bayan tashi daga barci. Sauran kusan kashi 20 cikin dari kuma a kullum, su kan sha tabar ne bayan awa daya da tashin su daga barci.

Wancan bincike ya fayyace cewa duk irin yawan tabar da wadannan mutane mashaya taba suke sha a ko wace rana, muddin sun kara gaggauta kunna tabar bayan tashi daga barci, barazanar kamuwa da ciwon kansar huhu ko a bakin su tana kara karuwa. Masu nazarin sun ce, in an kwatanta wadanda su kan sha taba bayan tsawon lokaci da tashi daga barci, masu shan taba dake kunna ta da zarar sun tashi daga barcin safe sun fi samun yawan sinadarin NNAL a jininsu. Kuma ana samun wannan sinadari na NNAL ne dake haifar da ciwon kansa daga tabar da aka sha. Kazalika yawan irin wannan sinadari a jinin mutum kan yi nuni ga hasashen barazanar kamuwa da ciwon kansar huhu.

Bugu da kari binciken ya shaida cewa yawan sinadarin NNAL da ke cikin jinin masu shan tabar, na da nasaba da tsawon lokacin da suka sha taba, da shekarunsu a duniya, da jinsinsu, da yawan taba da su kan sha da dai sauransu. Duk da haka masu nazarin sun tunatar da cewa, ban da batun lokacin da mutum ya fara shan tabar a rana, mai yiwuwa shan tabar da zarar mutum ya tashi daga barci da safe, na iya sanya hayakin tabar yin karfi da kuma kara shiga cikin huhunsu, ta yadda yawan sinadarin NNAL da zai samu zai karu a jininsu.

Duba da wannan, ana iya cewa mai yiwuwa ne a iya bambanta masu shan taba da suka fi fuskantar barazanar kamuwa da ciwon kansar huhu, ta lokacin da suke fara shan taba a ko wace rana, matakin da kuma zai bada damar taimaka musu tun da wuri. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China