Iyaye kan yi fatan cewa, 'ya'yansu zasu zamanto masu son cin abinci, to amma kuma masana sun yi gargadi da cewa, jarirai masu son yawan cin abinci, za su fi fuskantar barazanar samun kiba bayan da suka yi girma.
Kwanan baya, an gabatar da sakamakon sabbin nazari guda 2 da aka yi a karkashin bangaren sashen kula da yara kanana na mujallar hukumar masu binciken ilimin likitanci ta kasar Amurka. Masana daga jami'ar London ta kasar Birtaniya sun yi amfani da bayanan da suka shafi tagwayen da suka sha bamban da juna, amma jinsinsu iri daya ne, wadanda an haife su ne a shekarar 2007 a kasar Birtaniya. Masanan sun yi nazari kan dangantakar da ke akwai tsakanin gazawa wajen koshin abinci, matukar son cin abinci da zarar an gan su, da samun kiba.
Wannan nazari ya nuna cewa, a yayin da shekarunsu suka kai watanni 6 a duniya, jariran da ba su saurin koshi bayan cin abinci ko wadanda da zarar suka ga abinci, sai suna son ci, nauyinsu ya fi na 'yan uwansu yawa har da giram 650.Nazarin ya kuma nuna cewar a yayin da jariran suka kai watanni 15 a duniya kuma, nauyinsu ya fi na 'yan uwansu yawa har da giram 900 zuwa dubu 1. Masanan suna ganin cewa, ga alama jarirai masu son cin abinci su kan yi zaman rayuwa ba tare da fuskantar yawan matsaloli ba, amma yayin da suka yi girma, ya fi kyau iyayensu su lura da shin ko 'ya'yansu suna cin yawan abinci fiye da yadda suke bukata, ko kuma ba su koshi cikin sauri bayan da suka ci abinci, hakan zai haifar da saurin karuwar nauyinsu, wanda zai kawo illa ga lafiyarsu.
Bayan haka kuma, a cikin wani nazari na daban da aka yi, masana sun tantance bayanan da suka shafi yaran Birtaniya kusan 2,300 da aka haife su daga shekarar 1994 zuwa 1996. Sun kuma yi amfani da kwayoyin dabi'ar halitta guda 28 da aka tabbatar da amfaninsu na haddasa matsalar kiba wajen sa maki kan barazanar samun kiba, inda idan yara suka kara samun maki, sai za su kara fuskantar barazanar samun kiba kamar yadda iyayensu da kakanninsu suka yi sakamakon gadon dabi'un halitta.
Masanan suna ganin cewa, yaran da suka fi samun makin sun fi fuskantar matsalar samun kiba, sa'an nan kuma ba su koshi cikin sauri bayan da suka ci abinci.
Masanan sun yi bayani da cewa, sakamakon nazarinsu ya shaida cewa, yin nazari kan ko yara suna jin sun koshi cikin sauri ko kuwa suna daukar lokaci kamin suji yunwa, bayan da suka ci abinci wannan zai taimaka wajen yin rigakafin samun kiba ko ba da magani. Alal misali, ya fi kyau yaran da ba su koshi cikin sauri bayan da suka gama cin abinci, to sai su rage dan sauran da ya rage su ci abincin daga baya, saboda ya hana su kwalama, tare da yin kokarin magance bullowar abinci mai dadi a kewayensu.