Kwanan baya, masu nazari daga kasashen Jamus da Holland sun gabatar da sakamakon nazarinsu cewa, bayan da mutum ya kammala dukkan ayyukansa a yini, ya kan kalli shirye-shiryen telebijin ko kuma ya yi amfani da kayayyakin wasanni na zamani, domin samun hutan jiki da kuma kwakwalwa, amma dukkan wadannan ba za su taimaka masa samun isasshen hutu ba, sai ma ya kara masa gajiya da takaicin zuci
Wasu masu nazari daga jami'ar Mainz ta Jamus da kuma jami'ar Amsterdam ta Holland sun tambayi mutane 471 da suka amsa tambayoyi da suka ba su a rubuce. Inda suka gano cewa, bayan da mutane suka kwashe yini guda suna gudanar da ayyuka da dama ko kuma karatu, wadanda suka gaji kwarai da gaske daga cikinsu suna ganin cewa, kallon shirye-shiryen telebijin da wasa da kayayyakin wasanni na zamani kan bata lokaci, su kan hana su ci gaba da ayyukansu ko karatun da suke. Shakatawa a maimakon gudanar da abubuwa masu muhimmanci kan sanya wadannan mutane yin da na sani, a karshe kwakwalwarsu ba ta samu hutu ba.
Sakamakon nazarin ya shaida cewa,tunanin da ake na sassauta gajiyar da aka ji ta hanyar wasa da kayayyakin wasanni na zamani ba ta biya bukatar jiki ba. Wadanda a kullum suka dogara da amfani da kayayyakin nishadantarwa na zamani ba su cimma burinsu ba, ba su huta yadda ya kamata ba, saboda a ganinsu yin wasa kan dauke musu hankali. Masu nazarin sun yi bayani da cewa, a zamanin yanzu wayar salula ta zamani da yanar gizo ta Internet sun zama ruwan dare gama duniya, ga alama bayanan da ake samu cikin sauki da kuma mabambantan hanyoyin nishadi sun zama wa mutane babban nauyi da matsin lamba, a maimakon kyawawan hanyoyin sassauta gajiyar da aka ji.
Masu nazarin suna ganin cewa, sakamakon nazarinsu ya nuna cewa, a rayuwarmu na yau da kullum, akwai wata alaka mai sarkakiyya a tsakanin kayayyakin nishadantarwa na zamani da kuma koshin lafiyar mutane a bangaren tunani da kuma lafiyar jiki. Watakila mutane na bukatar kara yin tunani kafin su rika wasa da wayoyinsu na salula na zamani da kuma na'urar Ipad. (Tasallah)