in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mai yiwuwa kiba fiye da kima ta rage tsawon rayuwar mutane da kusan shekaru 14
2014-11-14 15:26:35 cri
Masu karatu, ko kun san cewa yawan kiba kan iya rage tsawon rayukanku! Wani sabon nazarin da aka yi a kasar Amurka ya nuna cewa, matsakaicin tsawon ran wanda mizanin awon nauyin jikin sa ko BMI a takaice ya wuce 40, bai kai na wanda mizanin BMI din sa ke daidai wadaida ba, a fannin samun tsahon rayuwa da kusan shekaru 14. Dalilin da ya sa hakan kuwa a cewar wancan bincike shi ne, masu yawan kiba su kan mutu da wuri sakamakon kamuwa da cutuka irin su kansa, da ciwon zuciya, da shanyewar jiki, da ciwon sukari, da ciwon hanta da dai sauran cututtuka cikin sauki.

Mizanin BMI, mizani ne na awon nauyin mutum a kilogiram a raba da tsayin mutum a mita sikwaya; kamar yadda hakan ke fayyace cikin awo irin na turawa wato weight (kg) / [height*height(M*M)]. Idan mizanin BMI na mutum ya zarta 18.5, amma bai wuce 24.9 ba, to, nauyin wannan mutum ya yi daidai. Amma idan mizanin BMI na mutum ya wuce 25 amma bai zarta 29.9, to, nauyin jikinsa ya dan wuce misali. Shi kuwa wanda mizanin BMI din sa ya wuce 30, amma bai zarta 39.9, ya na kan sahun masu kiba. Sai kuma wadanda mizanin su ya wuce 40, da aka sanya a ajin masu kibar da ta haura misali. Ma'anar mai kibar da ta haura misali ga wani mutum mai matsakaicin tsayi, ita ce nauyinsa ya dara nauyin wani mutum mai madaidaicin nauyin jiki fiye da kilogram 45.

Masu nazari daga cibiyar nazarin ciwon kansa ta kasar Amurka sun gabatar da wani rahoto dake cewa, sun tantance masu kibar da ta haura misali fiye da dubu 9 da dari 5, da masu madaidaicin nauyin jiki fiye da dubu 300 da suka fito daga kasashen Amurka, Sweden da Australia, inda suka gano cewa, ban da wadanda suke shan taba ko kuma wadanda suke fama da wasu cututtukan musamman, barazanar mutuwa da masu kibar da ta haura misali ke fuskanta na karuwa ne sakamakon karuwar mizanin BMI.

Galibi dai Idan mizanin BMI na mutum ya wuce 40 amma bai wuce 44.9 ba, to tsawon ransa kan ragu da shekaru 6 da rabi. Kuma idan mizanin BMI na mutum ya wuce 45 amma bai wuce 49.9, to tsawon ransa kan ragu da shekaru 8.9. Idan kuwa mizanin BMI na mutum ya wuce 50 amma bai wuce 54.9 ba tsawon ransa kan ragu da shekaru 9.8. Kana mizanin BMI na mutum wanda ya wuce 55 amma bai haura 59.9, ba na kan hasashen raguwar tsawon rai da shekaru 13.7.

Shin ko kun san cewa, shan taba kan rage tsawon ran mutane masu madaidaicin nauyin jiki da shekaru 8.9? Kana a iya cewa tara kibar da ta haura misali na da matukar illa ga lafiyar mutane.

Masu nazarin sun bayyana cewa, a baya kibar da ta haura misali ga mutane, wani ciwo ne da ba safai a kan kamu da shi ba. Ba ma a yin nazari kan barazanar mutuwa da wuri sakamakon kibar da ta haura misali. Amma a kwana a tashi, karin mutane na fama da shi a yanzu. Alal misali, a kasar ta Amurka, baligan da yawansu ya kai kashi 6 cikin dari ne suka shiga layin masu kibar da ta haura misali. Don haka ya zama tilas a mai da hankali kan matsalar kibar da ta haura misali.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China