in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana gaggauta nazari game da cutar Ebola
2014-10-05 15:43:43 cri

Ko da yake yanzu ana namijin kokarin yaki da cutar nan mai matukar hadari ta Ebola a yammacin nahiyar Afirka, kuma hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa wato WHO ta sha yin kiraye-kiraye ga kasashen duniya, da su mara wa kasashen Afirka baya wajen yaki da cutar. A hannu guda cutar ta Ebola, cuta ce da ba safai akan samu bullar ta ba, kuma sabili da haka ne ma likitoci ke kan mataki na farko wajen bai wa wadanda suka kamu da cutar jiyya yadda ya kamata.

Amma abin farin ciki shi ne labaran da aka samu daga sassa daban daban a kwanakin baya bayan nan, wadanda ke shaida cewa ana gaggauta nazari kan cutar ta Ebola.

Masana sun nuna cewa, tilas ne abi hanyar tantancewa a dakin gwaje-gwaje, domin a iya tabbatar da ko wani ya kamu da cutar ta Ebola ko a'a. Kuma a yanzu haka cibiyar kula da cututtuka ta kasar Amurka, da kuma ma'aikatar tsaron kasar sun fito da tsare-tsaren su guda biyu, na tabbatar da kamuwa da cutar, inda cikin awoyi masu yawa suka kai ga samun sakamako. Wadannan ma'aikata 2 sun hada kansu cikin himma da kwazo, suka shirin yin amfani da tsare-tsarensu a duk fadin kasar ta Amurka a nan da makonni da dama masu zuwa, da zummar ganin an iya tantance cutar a sassa daban daban na kasar.

A sa'i daya kuma, dakunan gwaje-gwaje na tafi-da-gidanka na Turai da kungiyar tarayyar Turai wato EU ta kafa, domin yaki da cututtukan da za ta iya yin bullar ba-zata, suna gudanar da aikinsu yadda ya kamata. Inda a watan Maris na shekarar 2014, aka tura irin wannan dakin gwaje-gwaje na farko zuwa gundumar Gueckedou dake kasar Guinea inda aka samu bullar cutar, kuma an yi amfani da shi wajen tabbatar da ko wani ya kamu da cutar ko a'a har sau 1100, ciki kuma fiye da sau 400 an tabbatar da kamuwar mutane da kwayar cutar.

A watan Agustar nan da muke ciki, kungiyar EU ta yi shirin kafa irin wannan dakin gwaje-gwaje na biyu. Wanda da shi ana iya tantance wasu nau'o'in munanan cututtukan da ke addabar mutane a dukkanin fadin duniya. Kuma kasancewar su dakunan gwaje-gwaje na tafi-da-gidanka, ana iya tura su zuwa wuraren da ke fama da cutar, wato ta hanyar amfani da irin wadannan dakunan gwaje-gwaje ana iya takaita halin musamman da kwayoyin cututtukan suke da shi, tare da samun bayanai da dumi-duminsu.

An labarta cewa, a farkon watan Agustar nan an maida Amurkawan nan su 2 zuwa gida, bayan da aka tabbatar sun kamu da cutar ta Ebola a kasar Liberia, kuma a 'yan kwanakin baya dukkansu sun warke sarai, sun kuma bar asibiti bayan da aka ba su magungunan da har yanzu ke matsayi na gwaji, wadanda kawo yanzu ba a sayar da su a kasuwa a hukumance, lamarin da ba shakka ya farantawa mutane rai sosai, ya kuma sanya likitoci, da ma dukkan al'ummar duniya samun haske, da hasashen samun nasarar yaki da cutar ta Ebola. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China