in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mai yiwuwa ne mata masu juna biyu dake fama da sankarar mama su iya amfani da hanyar magani ta Chemotherapy domin yaki da ciwon su
2014-11-17 17:36:44 cri

Sakamakon matukar damuwa kan illar da za a iya haifarwa jarirai, ya sa wasu mata masu juna biyu da ke fama da ciwon kansa ko sankarar mama, ke kaucewa amfani da sinadaran magunguna na zamani ko Chemotherapy a Turance ya yin da suke jiyya.

Sai dai a hannu guda asibitin kasa da kasa na Seiroka dake kasar Japan ya gabatar da sakamakon wani sabon nazarin da ya gudanar. Wanda ke nuna cewa muddin ciki ya kai watanni biyar, ko da mai dauke da shi ta yi amfani da sinadaran magunguna na zamani domin yaki da ciwon kansar mama, mai yiwuwa ne hakan ba zai kawo wata illa ga lafiyar jaririn da take dauke da shi ba.

Wannan asibiti ya yi nazari kan mata 34 da suka samu ciki daga shekarar 1999 zuwa shekarar 2013, wadanda kuma ke fama da ciwon kansar mama. Bayan watanni 5 da sumun juna biyun, wadannan mata sun fara yin amfani da sinadaran magunguna na zamani domin yaki da ciwon. A karshe dai, wasu 4 daga cikinsu sun fuskanci barazanar yin bari yayin da suka samu ciki, wasu 2 kuma sun kamu da ciwon sukari, wata kuma ta gamu da matsalar rashin isasshen ruwa a cikinta. Wasu 4 kuwa aka yi musu tiyata yayin da suka zo haifuwa.

Likitocin daga asibitin Seiroka na kasar ta Japan suna ganin cewa, yawan matan da suka gamu da matsaloli yayin da suka samu ciki daga cikin wadannan mata 34, ya yi kusa da adadin yawan wadanda suka gamu da matsaloli iri daya daga cikin mata masu koshin lafiya. Kana ya zuwa yanzu ba a gano ko 'ya'yan da wadannan mata 34 suka haifa suna tare da wasu matsaloli yayin da suke girma ba.

Wannan bincike dai ya shaida cewa, idan mace ta kamu da ciwon kansar mama kana ta samu juna biyu, bayan watanni 5 kuma ta fara amfani da sinadaran magunguna na zamani domin yaki da ciwon, yiwuwar faruwar illa ga lafiyar jaririnta ko jaririyarta sakamakon magungunan da take amfani da su na raguwa kwarai.

A ko wace shekara, Japanawa mata kimanin dubu 20 da shekarunsu suka haura 20 amma ba su wuce 49 a duniya ba su na kamuwa da ciwon kansar mama, wadanda yawansu ya kai kashi 27 cikin dari bisa jimillar wadanda suke kamuwa da ciwon. Karin wasu matan kuwa na kamuwa da ciwon ne yayin da suka samu ciki. A irin wannan hali babu abin da wasu daga masu juna biyun kan iya yi, illa su zubar da cikin a matsayin matakin jinya.

Sakamakon nazarin da likitocin Japan suka gabatar sun ba wa matan da ke fama da ciwon kansar mama wani zarafi na daukar ciki, da yin jinyar ciwon kansa yayin da suka samu ciki.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China