Wasu iyaye suna damuwa ganin yadda jariransu ba sa iya yin barci mai tsaho a wasu lokutan da suka sabawa dare.
Wani sabon nazarin da aka yi a kasar Australia ya gano cewa, wasu dabaru na kimiyya na da amfani sosai wajen taimakawa jarirai yin barci, kana kuma ba su da wata illa ga jariran yayin da suke girma.
Masu nazari a cibiyar nazarin lafiyar kananan yara ta Murdoch sun gabatar da wani rahoto dake nuna cewa, binciken su ya shaida cewa, bayan rabin shekara da haifuwar jarirai, wasu iyaye mata kusan 40 cikin dari ko fiye da haka, sun nuna damuwa kan matsalar barci da 'ya'yansu ke fama da ita, don haka wadannan iyaye mata kan fuskanci karuwar barazanar shiga cutukan da damuwa ke haddasawa. Sai dai binciken ya ce idan aka lallashi jariran da suka zarce watanni 7 a duniya yadda ya kamata, aka kuma nisanta su da inda iyayen su ke barci, hakan za a iya taimaka wa jariran yin barci da kyau.
Masu nazarin sun raba jarirai 225 da suka haura watanni 7 a duniya, wadanda ke fuskantar matsalar barci, zuwa rukunoni 2. Sun ba iyaye daga rukuni na A umarnin su lallashi jariransu yadda ya kamata, da kuma nisantar da kansu daga wurin da jariran suke barci, yayin da iyaye daga rukuni na B suka kasance da jariran na su.
Mene ne ma'anar lallashi jarirai yadda ya kamata? Ma'anar ita ce bayan dan lokaci, iyaye su lallashi jariran dake yin kuka, sa'an nan sannu a hakali su tsawaita lokacin, ta yadda jariran za su daina yin kuka da kansu. Ma'anar nisanta iyaye daga wurin da jariran su ke barci kuwa ita ce, a mataki-mataki iyaye su rika nisanta kansu daga wurin da jariran su kan yi barci, a karshe sai su bar dakin renon jariran, ta yadda jariran za su saba da yin barci da kansu.
A cikin binciken da masu nazarin suka yi shekaru 6 suna gudanarwa, sun yi bincike na rana-rana game da lafiyar iyaye da jariransu a fannonin motsin rai da halayyar su, sun kuma gano cewa jariran da aka taimaka musu wajen yin barci yadda ya kamata 'yan shekaru 1 zuwa 2 a duniya, barcinsu ya kyautata kwarai da gaske. Sa'an nan sakamakon binciken da aka yi musu cikin kusan shekaru 6, dangane da tunaninsu da kwarewarsu game da tinkarar matsin lamba ya shaida cewa, dabarun da aka yi amfani da su wajen taimakawa jarirai yin barci yadda ya kamata ba su kawo illa ga lafiyarsu a tunani da halayya ba yayin da suke girma.
A sa'i daya kuma, masu nazarin sun tunatar da iyaye da cewa, ana amfani da wadannan dabaru 2 wajen taimakawa jariran da shekarunsu suka wuce watanni 6 a duniya ne kawai, saboda wadannan jarirai sun san cewa, ko da ba su iya ganin iyaye da sauran abubuwa ba, su na sane da cewa iyayensu da sauran abubuwa suna tare da su. (Tasallah)