logo

HAUSA

Zazzabin Lassa ya kashe mutane 86 a Najeriya

2022-02-27 17:09:00 CRI

Hukumar dakile yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC, ta sanar cewa, adadin mutanen da cutar zazzabin Lassa ya kashe a bana a kasar ya kai 86, yayin da gwamnatin kasar ke ci gaba da daukar matakan rage yaduwar cutar.

A sanarwar da hukumar dakile cutuka ta kasar ta fitar, ta nuna cewa, an samu karin mutane 21 da cutar ta kashe, yayin da aka samu sabbin mutane 91 da suka kamu da cutar a kasar, tsakanin ranar 14 zuwa 21 ga watan Fabrairu.

Adadin hasarar rayukan da aka samu a kasar a sanadiyyar cutar a cikin wannan shekara, ya kai kashi 19.1 bisa 100, wanda ya yi matukar raguwa idan an kwatanta da adadin kashi 27.5 bisa 100 a makamancin lokacin shekarar 2021, a cewar hukumar.

Hukumar ta NCDC ta ce, tana ci gaba da nuna cikakken goyon bayanta ga tawagar jami’an hukumomin kiwon lafiya na jahohin kasar, domin cimma nasarar rage adadin masu kamuwa da cutar zazzabin Lassa zuwa kaso mafi kankanta a kasar.

A cewar hukumar, a halin yanzu, tana raba kayayyakin kula da lafiya ga asibitocin jahohin kasar da cibiyoyin kiwon lafiya, a matsayin wani bangare na matakan dakile yaduwar cutar.

A ranar 26 ga watan Janairu, hukumar NCDC ta sanar cewa, ta sake farfado da dukkan shirye-shiryenta na bangarori daban daban na ayyukan daukin gaggawa domin dakile cutar zazzabin Lassa a dukkan cibiyoyin yaki da cutuka dake fadin kasar.(Ahmad)

Ahmad