logo

HAUSA

Likitancin Gargajiyar Kasar Sin Ya Taimaka Wa Gu Ailing Eileen Ta Samu Lambar Zinariya

2022-02-09 21:28:02 CRI

Likitancin Gargajiyar Kasar Sin Ya Taimaka Wa Gu Ailing Eileen Ta Samu Lambar Zinariya_fororder_gu

Ranar 8 ga wata,‘yar wasan kasar Sin Gu Ailing Eileen, ta zama zakara cikin wasan freeski big air na mata, a gasar wasannin Olympics da ke gudana a birnin Beijing, inda karo na farko wata ‘yar wasan kasar Sin ta samu lambar zinariya a wasannin kankara mai taushi a gasar wasannin Olympics.

Gu Ailing Eileen, ta kafa tarihin ne bisa goyon bayan wani likitan kula da cututtukan da suka shafi kashi. A shekarar 2019, ta ji ciwo a kugunta bayan aikin horaswa. Dong Liangjie, wani likita ne mai kula da cututtukan da suka shafi kashi kuma mai ilmin likitancin gargajiyar kasar Sin, dake aiki a wani asibiti na lardin Henan, wanda ya yi mata jinya ta hanyar daidaita kashi. Gu Ailing Eileen ta sami sauki, ta kuma yi mamaki sosai game da tasirin likitancin gargajiyar kasar Sin. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan