logo

HAUSA

Babu wata fargabar zubewar ciki sakamakon karbar riga-kafin cutar COVID-19

2022-01-28 07:29:44 CRI

Babu wata fargabar zubewar ciki sakamakon karbar riga-kafin cutar COVID-19_fororder_u=1241943554,3359224784&fm=253&fmt=auto&app=138&f=JPEG(1)

Wani sabon binciken da aka wallafa a mujallar kiwon lafiya ta The New England Journal of Medicine ya nuna cewa, babu wata alaka tsakanin karbar allurar rigakafin cutar numfashi ta COVID-19 da barazanar zubewar cikin da ake dauke da shi.

Binciken ya yi nazarin wasu dakunan adana bayanan kiwon lafiya da dama a kasar Norway don kwatanta adadin matan da aka yi wa rigakafin wadanda suka samu zubewar ciki a yayin da ba su jima da daukar cikin ba da kuma matan da har yanzu suke da juna biyun bayan shafe watanni 3 na farko na daukar cikin.

Masu binciken sun bayyana cewa, “Binciken mu ya gano cewa, babu wani abun shaidar dake nuna cewa, akwai karuwar barazanar zubewar ciki a farko-farkon daukarsa, bayan da masu dauke da juna biyun suka karbi alluran riga-kafin cutar COVID-19. Sakamakon nazarin ya yi daidai da sakamakon da aka samu daga wasu rahotannin bincike dake nuna goyon bayan yi wa mata masu juna biyu rigakafin cutar COVID-19 yayin da suka dauki ciki.”

Sakamakon binciken yana kara ba da tabbaci ga matan da aka yi wa rigakafin a farkon daukar cikinsu kuma akwai karin abuuwan shaida dake goyon bayan cewa, yi wa mata masu juna biyu rigakafin cutar COVID-19 ba shi da wata illa.

Masu binciken sun gano cewa, babu wata dangantaka game da nau’o’in rigakafin cutar COVID-19 da kuma zubewar ciki. A kasar Norway, rigakafin da aka yi amfani da su sun hada da na kamfanin Pfizer, Moderna da AstraZeneca.

Manazartan sun rubuta cikin rahoton nazarinsu cewa, yana da muhimmanci a yi wa mata masu juna biyu rifa-kafin, saboda sun fi fuskantar yiwuwar kwanta a asibiti da kuma kamuwa da cututtukan da suka biyo bayan kamuwa da cutar COVID-19, kuma ‘yan tayin dake cikinsu sun fi fuskantar hadarin haihuwarsu da wurwuri.

Sannan binciken ya nuna cewa, yin rigakafin ga mata masu juna biyu mai yiwuwa ne zai iya samar da kariya ga jarirai sabbin haihuwa da suka haifa daga kamuwa da cutar COVID-19 a watannin farko-farko bayan haifuwarsu. (Ahmad)

Ahmad