logo

HAUSA

Kamuwa da COVID-19 ya kara kawo wa masu juna biyu barazana ga lafiyarsu

2022-01-10 14:56:09 CRI

Kamuwa da COVID-19 ya kara kawo wa masu juna biyu barazana ga lafiyarsu_fororder_src=http___bfttimg2.hebtv.com_p_2020-02-15_2bg2ate0h01&refer=http___bfttimg2.hebtv(1)

Wani nazarin da jami’ar Oxford ta kasar Birtaniya ta gudanar ya nuna cewa, kamuwa da annobar cutar numfashi ta COVID-19 ya kara kawo wa masu juna biyu barazana ga lafiyarsu da ma lafiyar jariransu sabbin haihuwa, sabanin zaton da aka yi a baya.

Wannan nazarin da ke karkashin shugabancin masana daga jami’ar Oxford ta kasar Birtaniya,ya nazarci masu juna biyu fiye da dubu 2 da dari 1 daga kasashe 18 na duniya. Masu nazarin sun tantance lafiyar masu juna biyu da suka kamu da cutar COVID-19 da kuma wadanda suke cikin koshin lafiya. Masu nazarin sun kaddamar da sakamakon nazarinsu cikin mujullar kungiyar ilmin likitancin kasar Amurka dangane da ilmin kula da kananan yara a ‘yan kwanakin baya.

Masu nazarin sun yi karin bayani da cewa, idan mata suka kamu da cutar COVID-19 yayin da suke da ciki, to, yiwuwar kamuwa da cututtukan da suke biyo bayan samun ciki za ta karu da kaso 50 cikin dari gare su, idan aka kwatanta da masu juna biyu wadanda ba su kamu da cutar ba. Kana kuma ko da yake masu juna biyu marasa yawa sun rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar ta COVID-19, idan masu juna biyu sun kamu da cutar, to, barazanar mutuwa da suke fuskanta yayin da suke dauke da ciki da kuma bayan haihuwa, ta ninka sau 22, in an kwatanta su da masu juna biyu wadanda ba su kamu da cutar ba.

Har ila yau kuma, masu nazarin sun yi bayani da cewa, idan masu juna biyu sun kamu da cutar COVID-19, to, jariransu sabbin haihuwa sun fi fuskantar barazanar kamuwa da cututtukan da suka biyo bayan kamuwa da cutar, har kusan sau 3, in an kwatanta su da takwarorinsu wadanda masu koshin lafiya suka haife su.

Dangane da lamarin, madam Zhang Chuji, wata likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, wannan sabon sakamakon nazari ya nuna mana cewa, illar da cutar COVID-19 take kawo wa masu juna biyu da jarirai sabbin haihuwa ta fi muni, sabanin yadda aka yi zato a farkon lokacin barkewar annobar cutar COVID-19 a baya. Sabili da haka ne ya kamata a yi la’akari da wannan batu yayin da ake daukar matakan dakilewa da kandangarkin annobar. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan