logo

HAUSA

Erastus Mwencha: BRI Ta Bunkasa Hadin Gwiwar Bangarori Daban Daban Da Ci Gaban Dukkan Bangarori

2021-12-19 21:17:01 CRI

Tsohon shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Afrika AU Erastus Mwencha, ya ce shawarar “ziri daya da hanya daya” wato BRI, wadda kasar Sin ta gabatar ta samar da wani dandalin bunkasa hadin gwiwar bangarori daban daban, da samun ci gaba mai kunshe da dukkan bangarori, da zaman lafiya da hadin kai.

Erastus Mwencha ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Juma’ar da ta gabata. Ya kara da cewa, ayyukan da ake gudanarwa karkashin shawarar ta ‘BRI’, sun hada da gina hanyoyin mota, layukan dogo, tashoshin jiragen ruwa da ababen more rayuwa na zamani, dukkansu sun kawo gagarumin sauyi ga kasashen Afrika da karfafa musu gwiwa wajen hadewa da juna da dunkelwar tsarin cinikayya.

Mwencha ya bayyana hakan ne a gefen taron tattaunawa na majalisar bada shawara kan hadin gwiwar kasa da kasa game da shawarar ‘ziri daya da hanya daya,’ ta kafar bidiyo.

Tsohon jami’in AU ya ce, gaggauta aiwatar da ayyukan more rayuwa ta fannin sufuri, da makamashi, da fasahar sadarwa karkashin shawarar BRI, ya rage tsadar kudaden gudanar da kasuwanci, baya ga samar da ayyukan yi a Afrika har ma kasashe masu tasowa baki daya.(Ahmad)

Ahmad