logo

HAUSA

Idan hulda ta yi tsami cikin iyali, to, za ta iya illa ga lafiyar yara a jiki da tunani da kwarewarsu ta yin magana

2021-10-11 09:01:14 CRI

Idan hulda ta yi tsami cikin iyali, to, za ta iya illa ga lafiyar yara a jiki da tunani da kwarewarsu ta yin magana_fororder_8326cffc1e178a82390552333693d98ba877e8fb

Wani nazarin da aka gudana a kasar Australiya ya gano cewa, idan kananan yara suna zama cikin iyalin da huldar da ke tsakanin mambobinta ta yi tsaimi bayan da aka haife su, to, sun fi takwarorinsu saukin gamuwa da matsala a fannonin yin magana, motsin rai da yin abubuwa.

Masu nazari daga kwalejin nazarin kananan yara na Murdoch na Australiya wato MCRI sun yi nazarin kan mata 1507 da suka haihu karo na farko daga asibitocin duba lafiyar mata guda 6 a birnin Melbourne da kuma ‘ya’yansu na farko, cikinsu kuma huldar da ke tsakanin rubu’insu da wadanda suke zama tare da su ta taba yin tsami har ma mizajensu sun ci zarafinsu a shekaru 10 na farko bayan haihuwa.

Masu nazarin sun gano cewa, idan ba a samu jituwa a tsakanin mambobin iyalan kananan yara bayan haihuwarsu ba, to, yiwuwar da suke fuskanta wajen gamuwa da matsala a fannonin tunani, motsin rai, yin abubuwa da yin magana za ta fi ta takwarorinsu yawa har sau biyu, kana kuma sun fi saukin kamuwa da ciwon asma da matsalar barci.

Haka zalika masu nazarin sun yi nuni da cewa, idan kananan yara suka gamu da matsalar lalacewar hulda a tsakanin mambobin iyalansu kafin su kai shekaru 5 da haihuwa, to, baya ga watakila za su kamu da ciwon asma da fama da matsalar yin magana, ba sa fuskantar matsala a lafiyarsu yayin da shekarunsu suka kai 10 a duniya, lamarin da ya shaida mana muhimmancin samun jituwa tsakanin mambobin iyalai.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, sakamakon nazarinsu ya nuna mummunar illar da lalacewar hulda tsakanin mambobin iyalai take kawo wa kananan yara. Mata da kananan yara sun fi saukin samun illoli daga lalacewar hulda a tsakanin mambobin iyalai wadanda suke zama tare, alal misali cin zarafinsu, ko kuma matsa musu lamba, musamman ma kananan yara, inda za su rika jin tsoro ko kuma nuna damuwa.

Dangane da lamarin, madam Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, sakamakon barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19, ya sa iyalai masu dimbin yawa kara fuskantar matsin lamba, lamarin da zai sa huldar da ke tsakanin mambobin iyalan wadanda suke zama tare ta fi saukin yin tsami. Don haka kamata ya yi hukumomin kula da lafiyar kananan yara da kuma biyan bukatun al’umma su fahimci illolin da kananan yara za su samu a tunani da jiki, su kuma ba da goyon baya da taimako ga mata da kananan yara wadanda suka gamu da matsala. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan