Kila rashin kwanciyar hankali tsakanin miji da mata zai kawo illa ga dabi'ar ‘ya’yansu
2021-11-08 16:29:06 CRI
Wani nazari da aka gudanar cikin hadin gwiwar wasu kasashe ya shaida cewa, idan miji da mata ba su samu kwanciyar hankali a tsakaninsu yayin da matar ta samu ciki ba, to, ‘ya’yansu za su fuskanci karuwar yiwuwar samun matsalar yanayin zuciya da ta dabi'a.
Masu nazari daga jami’ar Cambridge, da jami’ar Birmingham ta kasar Birtaniya da jami’ar New York ta kasar Amurka da jami’ar Leiden ta kasar Netherlands sun amince da hakan bayan da suka yi bincike kan masu juna biyu 438 wadanda suka samu ciki karo na farko da kuma mazajensu, wadanda suka fito daga kasashen Birtaniya, Amurka da Netherlands. Masu nazarin sun gayyaci ma'auratan da su rubuta takardar tambaya tare da yin hira fuska da fuska, yayin da aka cika watanni 28 da samun ciki har zuwa haihuwa, da lokacin da ‘ya’yansu suka cika watanni 4 da haihuwa, da watanni 14 da haihuwa, da watanni 24 da haihuwa. Tambayoyin da aka tanada cikin takardar sun hada da ko sun taba nuna damuwa da yin bakin ciki ko a’a. Yayin da masu nazarin suka yi hira da su fuska da fuska kuma, an ambato huldar da ke tsakanin ma'auratan, yanayin zuciyar ‘ya’yansu da dabi’arsu.
Sakamakon nazarin ya nuna cewa, dabi’ar kananan yara kafin shekarunsu su kai 2 da haihuwa ya danganta da yadda masu juna biyu wadanda suka samu ciki karo na farko suka yi farin ciki ko a’a kafin haihuwa. Idan masu juna biyu sun fuskanci babbar matsin lamba a tunani da babbar damuwa, to, ‘ya’yansu sun fi yiwuwar samun matsalar dabi’a kafin shekarunsu su kai 2 a duniya, alal misali yin fushi lokacin da suka ga dama da rashin kwanciyar hankali a tunani. Ban da haka kuma, idan ba a samu kwanciyar hankali tsakanin miji da mata ba a farkon lokacin da matar ta haihu, alal misali, dukkansu ba sa farin ciki, sun yi fada ko kuma sun yi rikici a tsakaninsu, to, ‘ya’yansu kan fuskanci karuwar yiwuwar saurin kuka da bakin ciki da jin tsoro kafin shekarunsu sun kai 2 a duniya.
Masu nazarin sun yi bayani da cewa, alkaluma sun nuna cewa, matsalar lafiyar tunani da ma’aurata suke fama da ita a lokacin samun ciki ta kan yi illa ga dabi’ar ‘ya’yansu, wadda ta sha bamban sosai.
Dangane da lamarin, madam Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, ko da yake karin abubuwan shaida sun nuna mana muhimmancin lafiyar tunanin masu juna biyu, nazarin da muka ambata a baya ya jaddada cewa, mizajen masu juna biyu suna bukatar ba da nasu goyon baya ga matansu, kana kuma wajibi ne a mai da hankali kan huldar da ke tsakanin sabbin iyaye. (Tasallah Yuan)
Labarai Masu Nasaba
- Yin rigakafin kamuwa da ciwon bakin ciki yayin da aka samu ciki
- Rayuwa ta hanyar da ta dace yana iya kare mutane daga kamuwa da ciwon karancin basira
- Manazarta sun gargadi matasa kan illolin yawan kallon kayayyakin laturoni na zamani na dogon lokaci
- Dangogin dangantakar jini kai tsaye na masu fama da yin tafiya yayin barci sun fi masu koshin lafiya fuskantar barazanar kamuwa da ciwon Parkinson's disease har sau 3 zuwa 6