logo

HAUSA

Sakatare Janar na MDD ya yaba da ka’idojin zaben shugaban Sao Tome and Principe

2021-09-04 16:16:54 CRI

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi maraba da rattaba hannu kan ka’idojin zabe da ‘yan takarar shugaban kasar Sao Tome and Principe suka yi dangane da zagaye na biyu na zaben kasar, yana mai kira da a warware rikice-rikice bisa hanyoyin shari’a.

Sanarwar da kakakinsa Stephane Dujarric ya fitar, ta ruwaito cewa, Antonio Guterres na bibiyar yanayin tsarin zaben shugaban kasar Sao Tome and Principe, kuma ya aminta cewa, an gudanar da zagaye na farko cikin lumana.

Sakatare Janar din ya kuma yi maraba da rattaba hannu kan ka’idojin zabe da ‘yan takarar shugabancin kasar biyu suka yi gabanin zagaye na biyu na zaben da za a yi gobe Lahadi, yana mai karfafa wa masu ruwa da tsaki gwiwar ci gaba da tattaunawa da kafa hanyoyin warware rikice- rikice bisa doka, da kuma kauracewa duk wani nau’i na tashin hankali.

Har wa yau, ya yi maraba da yunkurin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen tsakiyar Afrika game da taimakonta na samar da wata hanyar tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a kasar, ciki har da tura Manzon musammam. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha