logo

HAUSA

Ministan harkokin waje na kasar Sin ya gana da shugabannin kasar Sao Tome and Principe

2018-01-17 11:53:34 CRI

A jiya Talata ne, shugaban kasar Sao Tome and Principe Jose Reynaldo Carvalho ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi a fadarsa da ke Sao Tome, babban birnin kasar.

Wang Yi ya isar da gaisuwar shugaban kasar Sin Xi Jinping ga shugaba Carvalho, kuma ya ce, kasar Sin ta yaba da yadda shugaban ke martaba manufar kasar Sin daya tak a duniya, kuma tarihi ya tabbatar da cewa, yadda aka farfado da huldar jakadanci a tsakanin kasashen biyu ya dace da muradun kasashen da kuma al'ummarsu. Shekaru 20 da suka wuce wani bangare ne na bunkasuwar huldar da ke tsakanin kasashen biyu, a don haka kamata ya yi sassan biyu su kara kokari, don maido da abubuwan da suka rasa tare kuma da ciyar da huldar kasashen biyu gaba.

A nasa jawabin shugaba Mr. Carvalho ya ce, yana farin cikin ganin yadda aka maido da huldar da ke tsakanin kasashen biyu a kan hanyar da ta kamata, kuma kasar Sao Tome and Principe tana martaba manufar kasar Sin daya tak a duniya, haka kuma tana fatan huldar dake tsakanin kasashen biyu za ta ci gaba da karfafa.

Shi ma firaministan kasar Patrice Trovoada ya gana da Mr. Wang Yi a wannan rana. (Lubabatu)