logo

HAUSA

WHO: Matakan daidaito wajen raba rigakafin COVID-19 ba su taka kara sun karya ba

2021-03-23 10:28:40 CRI

Babban darektan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce har yanzu ba a aiwatar da matakan raba rigakafin cutar COVID-19 daidai wa daida ba, wanda hakan ko alama bai dake ba.

Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana hakan ne, yayin taron manema labarai na jiya Litinin, yana mai kira da a hanzarta cike gibin adadin rigakafin da kasashe masu wadata ke yiwa al’ummun su, da kuma wadanda ake samarwa kasashe marasa wadata karkashin shirin nan na COVAX.

Har ila yau, babban jami’in na WHO ya kara kira ga kasashe mawadata, da su raba rigakafin da suke da shi da sauran sassan duniya karkashin shirin nan na COVAX, kana su ma kamfanonin dake sarrafa rigakafin su fadada samar da shi, ta yadda za a iya daidaita rabon sa tsakanin sassan duniya daban daban.

Shirin COVAX wanda ke gudana karkashin lemar WHO da abokan huldar ta, an tsara shi ne da nufin tallafawa kasashe masu rangwamen karfi, ta yadda za su samu rigakafin cutar COVID-19 cikin sauki, kuma shirin na kara samun karin tagomashi a kullum.  (Saminu)

Saminu